Duk da Ya Samu Digirin PhD, Sarki Sanusi Ii Ya Koma Jami'ar Kano Ya Yi Karatu
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu gurbin karatun digirin lauya (Common Law da Shari’a) a Jami’ar Northwest, Kano
- Jami’ar ta ba shi gurbin shiga mataki na biyu na karatun LL.B na shekarar karatu ta 2024/2025, duk da cewa ya kai matakin karatu na PhD
- Sanusi II wanda yake da digiri tun 1980s a ilmin tattalin arziki ya nuna wa duniya muhimmancin neman ilmo ko a shekarun girma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya samu gurbin karatu a Jami’ar Northwest da ke Kano domin karo ilimi.
Mai martaba Sarkin Kano ya samu gurbin karantar digirin lauya na a bangaren Shari'a, matakin da ya dauki hankalin jama’a a fadin kasar nan.

Source: Twitter
Adnan Mukhtar Tudun Wada ne ya bayyana haka a cikin wata wasikar samun gurbin karatun Sarki Muhammadu Sanusi II da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sarki Muhammadu Sanusi II zai koma makaranta
A sakon, an iya ganin wasika daga Daraktan Jarrabawa, Shiga Jami’a da Rijista (DEAR) na jami’ar da ta tabbatar da cewa an ba Sarkin gurbin shiga karatun LL.B Common a aji na biyu, domin shekarar karatu ta 2024/2025.
Wasiƙar, wacce ke dauke da kwanan wata 12 ga Janairu, 2026, ta bayyana cewa an amince da bukatar Sarkin ne bayan ya cika dukkannin sharuddan da jami’ar ta tanada domin ba da gurbi na musamman.
Adnan wanda ya yi karatu a jami'ar ta Northwest kuma yanzu haka yake digirin PhD a ilmin addinin Musulunci ya yi alfahari da ganin Mai martaba zai yi karatu a makarantarsu.

Source: Twitter
Takardar ta kara da cewa wannan amincewa tana karkashin bin dokoki da ka’idojin da ke kunshe a cikin kundin taron tafiyar da dalibai na jami'ar Northwest.
Haka kuma, an shawarci Sarkin da ya kammala dukkannin matakan rijista da suka hada da sashen DEAR, bangaren ICT, da kuma sashen kula da harkokin dalibai.
Ra'ayin jama'a game da karatun Sarki Sanusi II
Tuni masu bibiyar sahar ta Facebook suka fara mayar da martani da fadin albarkacin bakinsu game da shirin Khalifa Muhammadu Sanusi na komawa karatu.
Abubakar Isyaku ya bayyana cewa:
"Lallai, ba a daina koyo a duniya, In Sha Allah zan koma jami'a na karanci abin da zai karanta."
Nura Usman tambaya gare shi, inda ya ce:
"Zai rika zuwa daukar karatu, kuma zai rika kaya fari da baki ko"?
Mubaraq Usman Sadiq ya ce:
"Sunan na kama da sunan 'dansa."
Sarki ya yi wa 'yan siyasa tonon silili
A baya, mun wallafa cewa Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya yi kakkausar suka kan halin ’yan siyasa a Najeriya, yana zarginsu da hana ci gaban kasa da gangan.
Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin cika shekaru 15 na kungiyar Enough is Enough (EiE) Nigeria, wanda aka gudanar a Legas ranar Laraba, 10 ga Disamban 2025.
A cewarsa, manyan ’yan siyasa sun kauce wa damammaki masu muhimmanci da za su iya habaka kasa, saboda suna kallon mukaman gwamnati a matsayin hanya ta amfanin kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

