Akwai Matsala: Gwamnatin Tarayya Ta Gamu da Cikas a Shirin Aiwatar da Dokar Haraji

Akwai Matsala: Gwamnatin Tarayya Ta Gamu da Cikas a Shirin Aiwatar da Dokar Haraji

  • Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin raba ka'idojin aiwatar da dokar haraji, wacce ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairu, 2025
  • Shugaban kwamitin gyaran harajin shugaban kasa, Taiwo Oyedele ya ce za su jira Majalisa ta kammala bitar takardun dokokin harajin
  • Hakan na zuwa ne bayan zargin banbancin da aka samu tsakanin dokar da Majalisa ta amince da ita da wacce ke hannun gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta dakatar da bayar da ka’idojin aiwatar da sababbin dokokin haraji na kasa, saboda rashin tabbas kan ainihin dokar da aka amince da ita.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Taiwo Oyedele, Shugaban Kwamitin Gyaran Haraji na shugaban kasa.

Shugaban kwamitin haraji, Taiwo Oyedele.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan harkokin kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele Hoto: @TaiwoOyedele
Source: Twitter

A rahoton Daily Trust, Oyedele ya ce ya umurci Hukumar Haraji ta Kasa (NRS) da Hukumar Hadin Gwiwa ta Haraji (JRB) da su jira tukunna, domin ba za a iya fitar da ka’idojin aiwatar da dokokin harajin ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sayo dankara dankaran motoci 65 na alfarma, ya rabawa sarakuna

Ya bayyana haka ne a Legas jiya yayin da yake amsa tambayoyi bayan ya gabatar da jawabi a taron duba yanayin tattalin arziki na shekarar 2026, wanda Kungiyar Akantoci ta Najeriya (ICAN) ta shirya.

Dalilin dakatar da raba ka'idojin haraji

Oyedele ya ce babu tabbacin ko takardun da ke yawo a halin yanzu su ne ainihin dokar, wanda hakan ya sa ya tura ma’aikatansa su sayo kwafin dokar daga ma’aikatar buga takardu ta gwamnati.

Sai dai ya ce rahoton da ma’aikatansa suka dawo masa da shi ya nuna cewa Majalisar Dokoki ta Kasa ta karbe duka kwafin dokokin da aka buga, kuma ta hana sayarwa ko a bai wa jama’a su har sai ta kammala bita.

"A bisa tanadin doka, duk abin da ma’aikatar buga takardu ta gwamnati ta wallafa, shi ne shaida na sahihiyar dokar da aka kafa.
"Gwamnati ta buga wani kwafin dokar haraji, amma ‘yan majalisa suka ce ba abin da suka amince da shi ba ne. Don haka suka ce za su fitar da dokar da suka sani," in ji Taiwo Oyedele.

Me yasa Majalisa ta dauki wannan mataki?

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Tinubu ta yi wasu sauye sauye da sababbin dokokin haraji

Duk wani lokarin jin ta bakin mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, bai ci nasara ba, domin bai amsa kiran waya ko sakon WhatsApp ba.

Haka kuma, kiran da aka yi wa mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, bai shiga ba har zuwa daren jiy, kamar yadda Punch taa rahoto.

Majalisar wakilan Najeriya.
Zauren Majalisar wakilan tarayya a daidai lokacin da mambobinta ke tsakiyar zama Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Duk da ya yarda cewa bitar majalisa abu ne da aka saba yi a tsarin samar da doka, Oyedele ya lura cewa hana raba takardun ya sake haifar da rashin tabbas a tsarin gyaran harajin.

Ya kara da cewa:

“Na gaya wa duk wanda ya kamata, su ma hukumlmin NRS da JRB dole su jira, domin ba za mu iya fitar da ka’idoji ba.
"Ba mu da yakinin kashi 100 cikin 100 cewa wannan shi ne matsaya ta karshe kan dokar. Na gaya wa ma’aikatana su koma su zauna har sai sun samu takardun."

Bankuna za su fara cire harajin VAT

A wani rahoton, kun ji cewa bankunan kasuwanci da kamfanonin hada-hadar kudi ta intanet irinsu Moniepoint za su fara karbar harajin VAT daga abokan hulda.

Kara karanta wannan

Shugaban kwamitin harajin Tinubu na tsaka mai wuya, an fara barazanar tura shi lahira

Wannan sanarwa ta fito ne ta hanyar sakonnin imel da wasu kamfanonin hada-hadar kudi irin su Opay, PalmPay da Moniepoint suka fara aikawa abokan cinikinsu.

Za a rika cire wannan haraji ne a abin da bankuna ke dauka idan mutum ya tura kudi ko wata mu'amala ta intanet amma ba za a taba asalin kudin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262