Gwamnatin Kano Ta Gabatar da Bukatar Cafko Abdullahi Ganduje, Kotu Ta Yi Hukunci
- Kotun jihar Kano ta ki amincewa da bukatar kamo tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan zargin karkatar da hannun jarin tashar Dala
- Ana zargin Dr. Ganduje da mallaka wa yayansa guda uku hannun jarin gwamnati da kuma karkatar da Naira biliyan hudu na jama'a
- Wannan shari'a tana ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen shari'a da tsohon gwamnan na Kano yake fuskanta tun bayan barinsa ofis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Wata babbar kotun Jihar Kano ta ƙi amincewa da buƙatar bayar da sammacin kamo tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin Kano ce ta bukaci a kamo Dr. Abdullahi Ganduje kan zargin da ake masa na karkatar da mallakar filin tashar tsandauri da ke Dala.

Source: Facebook
Gwamnatin Kano ta yi karar Abdullahi Ganduje
Wannan hukunci ya zo ne a matsayin sassauci na ɗan lokaci ga tsohon gwamnan da sauran waɗanda ake tuhuma tare da shi a cikin wannan badakala ta mallakar hannun jari, in ji rahoton Premium Times.
Gwamnatin Jihar Kano ta shigar da Ganduje kara gaban kotu tare da hadiminsa, Abubakar Bawuro; lauyansa, Adamu Aliyu-Sanda; da kuma tsohon Babban daraktan hukumar Shippers’ Council, Hassan Bello.
Ana tuhumar su ne da laifuffuka guda 10 da suka haɗa da haɗin baki don yin zamba, karkatar da kuɗaɗen jama'a, cin amanar ƙasa, da kuma amfani da ofis don amfanin kai.
Rigimar ba da umarnin kamo Ganduje
A zaman kotun na ranar Laraba, 14 ga watan Janairu, 2026, lauyan gwamnati, Ya’u Adamu, ya bayyana wa kotun cewa wajibi ne a bayar da sammacin kamo Ganduje da sauran mutanen.
Ya bayar da hujjar cewa tun da waɗanda ake tuhumar sun ƙi bayyana a gaban kotu da kansu, to ya kamata alkali ya yi amfani da sashi na 388 na dokar gudanar da shari'ar manyan laifuka ta Jihar Kano don tilasta bayyanarsu.
Sai dai, Alkali Yusuf Ubale na babbar kotu mai lamba 2, ya yi watsi da wannan buƙatar kamar yadda rahoton ya nuna.

Kara karanta wannan
Mutum 2 da za su gabatar da shaida a shari'ar Ganduje sun fara fuskantar hadari a Kano
Alkalin ya bayyana cewa bayar da sammacin kamo wadanda ake tuhuma a wannan mataki zai kasance garaje da gaggawa.
Lauyan wadanda ake kara, A.S. Gadanya (SAN), ya ƙalubalanci buƙatar gwamnati, inda ya gabatar da hujjojin cewa akwai wasu ƙorafe-ƙorafe na shari'a da ya kamata kotu ta fara saurara kafin a fara karanta tuhume-tuhume.
Saboda wannan saɓani, kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: Facebook
Yadda aka karkatar da hannun jarin tashar Dala
Binciken da gwamnatin Kano ta gudanar ya nuna cewa Ganduje ya yi amfani da ofishinsa wajen karkatar da kashi 80 na hannun jarin tashar tsandauri ta Dala zuwa hannun masu zaman kansu ta hanyar wani kamfani da ake zargin na bogi ne mai suna “City Green Enterprise”.
Rahoton binciken ya nuna wani babban abin mamaki, na yadda aka fitar da gwamnatin jihar Kano daga cikin mallakar aikin gaba ɗaya.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa:
- A watan Maris na 2020, an nada ’ya’yan Ganduje guda uku—Abdulaziz, Umar, da Muhammad Abdullahi Umar—a matsayin daraktoci da masu hannun jari.
- Kowanne daga cikin yaran nasa an ba shi hannun jari miliyan biyar, wanda ke wakiltar kashi 20 cikin ɗari na dukkan hannun jarin kamfanin.
Gwamnatin jiha ta zargi Ganduje da karkatar da sama da Naira biliyan 4.49 na kuɗin jihar wajen gina hanyoyi, samar da wutar lantarki, da katange filin don amfanin kansa da iyalinsa.
Wannan shari'a tana ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen shari'a da tsohon gwamnan yake fuskanta tun bayan barinsa ofis.
Gwamnatin Abba na so a kama Ganduje
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sake taso tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin ta nemi a kama kuma a binciki tsohon gwamnan bisa zargin yin maganganun da ka iya tayar da tarzoma da kuma kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro a jihar Kano.
Ta kuma yi kira ga manyan ’yan siyasa da su guji kalaman da za su iya haifar da tashin hankali ko kara dagula matsalar tsaron da ake fama da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

