Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Sabon Tsari, Masu Amfani da Banki Za Su Fara Biyan VAT
- Bankunan kasuwanci da kamfanonin hada-hadar kudi ta intanet irinsu Moniepoint za su fara karbar harajin VAT daga abokan hulda
- Gwamnatin tarayya ce ta ba da umarnin fara cire harajin na kashi 7.5 na ladar aika kudi daga ranar Litinin, 19 ga watan Janairu, 2025
- Za a rika cire wannan haraji ne a abin da bankuna ke dauka idan mutum ya tura kudi ko wata mu'amala ta intanet amma ba za a taba asalin kudin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Daga ranar Litinin, 19 ga watan Janairu, 2026, daukacin bankunan kasuwanci da kamfanonin hada-hadar kudi na intanet za su fara cire harajin VAT na kashi 7.5 daga asusun 'yan Najeriya.
Wannan sanarwa ta fito ne ta hanyar sakonnin imel da wasu kamfanonin hada-hadar kudi irin su Moniepoint suka fara aikawa abokan cinikinsu a ranar Laraba.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ce gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Karbar Haraji ta Kasa (NRS), ce ta ba da umarnin fara cire harajin daga kudin caji da bankuna ke dauka.
Wadanne hada-hadar kudi ne harajin zai shafa?
Harajin na VAT ba zai shafi ainihin kudin da mutum ya tura ba, sai dai zai hau kan kudin da banki ke cirewa wajen gudanar da wadannan ayyuka.
Kudin da za a dauki harajin VAT daga cikinsu sun hada da:
- Cajin tura kudi ta waya.
- Kudaden hada-hadar amfani da lambobin sirri (USSD).
- Kudaden karbar sabon katin cirar kudi (ATM).
Misali: Idan banki yana cire N100 a matsayin cajin tura kudi, to za a kara cire kashi 7.5% na wannan N100 din (wato N7.50) a matsayin harajin VAT da za a tura wa gwamnati.
Abubuwan da harajin ba zai shafa ba
Sanarwar ta bayyana cewa har yanzu akwai ayyukan da aka amince ba za a cire musu harajin ba, wadanda suka hada da, kudin ruwa da kudin da mutum ya tara a asusun ajiya, cewar rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan
Jigon ADC ya zargi Tinubu da sakaci, an tsunduma mutane miliyan 141 a bakin talauci
A sakon da lamfanin Moniepoint ya tura wa wakilinmu, ya nanata cewa wannan mataki ba karin kudi ba ne daga bangarensu, face bin dokar kasa da ta wajabta musu karbar harajin da kuma mika shi ga hukumar NRS.

Source: Twitter
Wannan sabon tsari na daya daga cikin kokarin gwamnati na dunkule tsarin karbar haraji a harkar hada-hadar kudi ta intanet, domin fadada hanyoyin samun kudin shiga da nufin bunkasa tattalin arzikin zamani na Najeriya.
Idan za a iya tunawa, a watan Disamba ma bankuna sun sanar da abokan cinikinsu cewa za a ci gaba da cire kudin harajin Stamp Duty na N50 a duk lokacin da suka tura N10,000 ko fiye da hakan, sakamakon fara aikin sabuwar Dokar Haraji.
An yi gyara a dokokin harajin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kananun sauye-sauyen da aka samu ba za su rage komai a sababbin dokokin haraji ba.
Shugaban kwamitin sake fasalin haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taro da ya halarta a jihar Legas.
Ya bayyana cewa duk da hayaniyar da ake yi na cewa an sauya wasu abubuwa, wadancan sassa ba su da yawa kuma ba su taba muhimman batutuwan haraji da suka shafi al'umma ba.
Asali: Legit.ng
