Bidiyo: Yadda Gobara Ta Tashi Ana tsakiyar Sauke Fetur a Wani Gidan Mai a Kano
- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da afkuwar gobara a wasu gidajen mai biyu a Kano, da suka jawo asarar dukiya mai yawa
- Rahoto ya nuna cewa gobarar ta tashi ne a yayin da ake sauke man fetur a gidajen mai na AA Ayagi da Al-Wahida da ke a sassan jihar
- Wani bidiyo da Legit Hausa ta gani ya nuna lokacin da wuta take cin tankar mai gadan-gadan, yayin da hukuma ta jero asarar da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar kashe gobara ta Kano ta tabbatar da cewa mummunar gobara ta tashi a wasu gidajen mai biyu, a lokuta daban daban a ranar Talata, 13 ga Janairu, 2025.
Hukumar ta ce akalla baburan keke-napep guda 17 da tankokin dakon man fetur biyu ne suka ƙone kurmus sakamakon iftila'in da ya afkuwa a gidajen man biyu.

Source: Twitter
Gobara ta tashi ana tsakiyar sauke fetur
Waɗannan hadurra sun faru ne a yayin da ake sauke man fetur daga cikin tankokin, wanda hakan ya haddasa asarar dukiya mai ɗinbin yawa a jihar, in ji rahoton Channels TV.
Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa gobarar farko ta tashi ne a gidan man AA Ayagi da ke ƙauyen Kanye a kan hanyar Gwarzo.
Wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 8:45 na dare yayin da wata tankar fetur mai lamba XPB 999 FA take sauke man da ta dauko.
Hukumar ta ce duk da ƙoƙarin jami'an kwana-kwana na shiyyar Rijiyar Zaki, tankar man ta ƙone kurmus bayan ta sauke kashi biyu kawai na man da ke cikinta.
Barnar da gobara ta yi a sassan Kano
Jaridar Punch ta rahoto cewa, gobarar ta biyu ta faru ne a gidan mai na Al-Wahida Nigeria Limited da ke unguwar Rimin Kebe a ƙaramar hukumar Nassarawa.

Kara karanta wannan
An dakatar da likitoci kan barin almakashi a cikin matar aure yayin tiyata a Kano
A wannan karon ma, wutar ta tashi ne yayin da wata tankar mai ɗauke da lita 45,000 na fetur take sauke mai. Wutar ta yi barna sosai ind ta ƙone kan tankar da wani ɓangare na jikinta, sannan ta babbake baburan keke-napep guda 17.
Bayan waɗannan masifu, an kuma samu rahoton wata gobarar a unguwar Kundila Quarters, inda wuta ta lalata ɗaki guda, banɗaki, da barandar wani gidan zama kafin a shawo kanta.

Source: Original
Gargadi daga hukumar kashe gobara
Babban daraktan rundunar kashe gobara ta jihar, Sani Anas, ya yi kira na gaggawa ga masu gidajen mai da direbobin tankokin mai da su kiyaye dukkan matakan tsaro yayin sauke man fetur.
Ya jaddada cewa bin ƙa'idodin tsaro shi ne kaɗai zai iya hana aukuwar irin waɗannan manyan asarori na dukiya da za su iya shafar rayukan jama'a.
Hukumar ta bayyana cewa an yi nasarar ceto wasu sassan tankokin da kuma man fetur ɗin kafin wutar ta mamaye komai, inda ta yabawa jami'anta kan yadda suka nuna kwarewa wajen hana wutar bazuwa zuwa gidajen mutane.
Kalli bidiyon gobarar gidan man AA Ayagi, da wani Mustapha ya wallafa a shafinsa na Facebook, a nan kasa:

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun mamayi jami'an tsaro, sun kashe tsohon 'dan takarar majalisa da mutum 4
Gobara ta tashi a babbar kasuwar Kano
A wani labari, mun ruwaito cewa, wata gobara da ta tashi a kasuwar kayan masarufi ta Singa da ke jihar Kano ta jefa 'yan kasuwa a cikin dimuwa.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar faruwar lamarin, inda ta yi zargin cewa lamarin ya sakamakon kuskuren amfani da makunnin wuta.
Ginin mai hawa ɗaya da shaguna sama da 40 ne ya kama da wuta, lamarin da ya sa aka nemi ahajin jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Kano.
Asali: Legit.ng
