Bidiyo: Wani Dan Najeriya Ya Tada Rigima a Coci, Ya Fice daga Addinin Kiristanci

Bidiyo: Wani Dan Najeriya Ya Tada Rigima a Coci, Ya Fice daga Addinin Kiristanci

  • Wani dan agaji ya yi ridda daga addinin Kiristanci sakamakon rashin ambaton sunan dan siyasa a lokacin bude sabuwar coci a Anambra
  • An rahoto cewa marigayi Sanata Ifeanyi Ubah ya kammala 80% na aikin ginin cocin a 2022 amma aka ki ambatar sunansa a wajen bude majami'ar
  • Mutumin ya cire kayan agajinsa yana kururuwa yana cewa daga ranar ya fice daga Kiristanci, kamar yadda aka gani a cikin wani bidiyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Wani dan agajin cocin Katolika, Sir James Louise, wanda aka fi sani da Ebube Anaedo, ya sanar da yin ridda daga addinin Kiristanci a bainar jama'a.

Wannan mataki ya biyo bayan zargin da ya yi wa cocin Katolika na gaza karrama gudunmawar da marigayi Sanata Ifeanyi Ubah ya bayar wajen gina babban cocin "Our Lady of Assumption Cathedral" da ke Nnewi, jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Neman sulhu: Ƴan bindiga sun gindaya wa gwamnatin Katsina sharudda 8 masu tsauri

Wani mutumi ya tayar da rigima a coci lokacin da aka ki ambatar wani dan siyasa, ya fice daga Kiristanci.
Ginin coci babu kowa a ciki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rikici ya balle wajen bude coci

An buɗe katafaren cocin ne a ranar Laraba, 14 ga watan Janairu, 2026, a wani babban biki da ya samu halartar manyan mutane, in ji rahoton Arise News.

Rahotanni sun nuna cewa Ifeanyi Ubah ne ya ƙaddamar da aikin ginin kuma ya kammala kusan kashi 85 na aikin gina cocin kafin zuwan sabon Bishop, Jonas-Benson Okoye, a shekarar 2022, wanda aka ce ya dakatar da Ubah daga ci gaba da aikin.

Rikici ya ɓalle ne yayin bikin buɗe cocin, inda Sir James Louise, sanye da kayan agajinsa na Katolika, ya nuna fushinsa bayan an kammala addu'o'i.

Dan agajin coci ya fice daga Kiristanci

Ya koka da cewa ba a ambaci sunan Ifeanyi Ubah ba, ko ta baki ko a cikin takardun tarihin cocin, duk da irin maƙudan kuɗaɗen da ya kashe wajen ginin.

A cikin wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ga dan agajin yana kruruwa inda ya ce:

Kara karanta wannan

"Ina ya shiga?" Peter Obi ya fito da damuwarsa game da yawan tafiye tafiyen Tinubu

“Wannan ita ce ranata ta ƙarshe a matsayin Kirista. Na gama.
"Ta yaya za a buɗe wannan cocin ba tare da an ambaci sunan Ifeanyi Ubah wanda ya sha wahala wajen gina shi ba? Wannan abin kunya ne.”

Daga nan ya cire takalmansa da hularsa ta agaji a matsayin alamar barin addinin Kiristanci, cewar wani rahoto na Punch.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Wani dan agajin coci ya bar Kiristanci saboda marigayi Sanata Ifeanyi Uba.
Zauren majalisar dattawa da hoton marigayi Sanata Ifeanyi Uba. Hoto: @NGRSenate, @IgboHistoFacts
Source: Twitter

Martanin jama'a da shirun cocin

Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a yanar gizo, inda mutane da dama ke sukar cocin kan abin da suka kira rashin adalci ga marigayin.

Mutane da dama sun nuna cewa ya kamata a ba wa kowa hakkinsa ba tare da la'akari da sabani na siyasa ko na cikin gida ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, mahukuntan cocin Katolika na Diocese ta Nnewi ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba domin yin bayani kan dalilin da ya sa ba a ambaci sunan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah a matsayin wanda ya gina cocin ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Fastoci 2 da 'yar fasto sun bar Kiristanci

A wani labari, mun ruwaito cewa, tun daga karni na 15, Kiristanci ya zama babban addini a Najeriya, inda ke da manyan mazhabobi masu yawan mabiya.

Duk da cewa mutane da dama suna ci gaba da rungumar Kiristanci, an samu wasu ‘yan Najeriya da suka yanke shawarar barin addinin bayan bincike da tunani mai zurfi.

Daga cikin wadanda suka bar Kiristanci, akwai Abraham Daniel, wani fasto a cocin Dunamis ta Dr. Pastor Enenche, sannan akwai wata ‘yar fasto mai suna Shalom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com