Tashin Hankali: Wani abu da Ake Zargin Bam ne Ya Tarwatse da Mutane a Adamawa
- Mutane shida sun ji rauni a jihar Adamawa sakamakon fashewar bam da ake zargin yan ta'addan Boko Haram ne suka dasa a kauyen Mubang
- Shugaban karamar hukumar Hong ya yi kiran gaggawa ga gwamnatin tarayya domin tura dakarun sojin sama su fatattaki yan ta'adda a Sambisa
- Wannan na zuwa ne yayin da Bello Turji ya raba mutanen kauyuka kusan 20 da gidajensu a jihar Sokoto wanda hakan ya janyo kuncin rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Hukumar gudanarwa ta ƙaramar hukumar Hong da ke jihar Adamawa ta tabbatar da tashin wani abu da ake kyautata zaton cewa bam ne.
Karamar hukumar ta ce aƙalla mutane shida ne suka samu rauni sakamakon fashewar wani bam da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa shi a ƙauyen Mubang.

Source: Original
Wani bam ya tarwatse da mutane a Adamawa
Wannan harin na zuwa ne mako guda bayan da ’yan ta’addan suka kai wani mugun hari a ƙauyen, inda suka hallaka mutane 14 a farkon wannan watan na Janairu, 2026, in ji rahoton Punch.
Shugaban ƙaramar hukumar Hong, Usman Inuwa, ya bayyana wa manema labarai a ranar Laraba, 14 ga Janairu, 2025 cewa ba a rasa rai ba a wannan sabon harin.
Sai dai, Usman Inuwa ya bayyana cewa fashewar bam din ta jikkata mutane da dama waɗanda yanzu haka suke asibiti suna karɓar magani.
Ciyaman din ya kara da cewa ƙauyukan yankin suna kusa da dajin Sambisa, inda babu wasu garuruwa a tsakaninsu da dajin, wanda hakan ke ba ’yan ta’adda damar kai hari wuraren da babu jami'an tsaro.
Bukatar tallafin sojojin sama da na kasa
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa dakarun soja da na sa-kai na iyakar ƙoƙarinsu, inda ya bayyana cewa a cikin watan Disambar da ya gabata, Boko Haram sun yi yunƙurin kai hari sau uku amma aka dakile su.

Source: Facebook
Sai dai ya jaddada cewa ba za a iya kawo ƙarshen wannan matsala ba har sai idan rundunar sojin sama ta tura jirage don luguden wuta a maɓoyar ’yan ta’addan dake cikin daji, in ji rahoton The Guardian.
Usman Inuwa ya ce:
"Sai dai idan an tura sojin sama sun kai hari, sannan an girke sojoji na ƙasa a kusa, sannan za a samu sauƙin waɗannan hare-hare."
Bello Turji ya jefa mutane a damuwa
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, al'ummar gabashin jihar Sokoto sun yi kukan neman ɗauki bayan da fitaccen ɗan fashin daji, Bello Turji, ya raba mazauna ƙauyen Tidibale da wasu ƙauyuka kusan 20 da gidajensu.
Sakataren ƙungiyar ci gaban yankin gabashin Sokoto, Muazu Shamaki, ya tabbatar da cewa bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna yadda mutane ke guduwa daga gidajensu sakamakon barazanar Turji gaskiya ne.
Wannan lamari ya jefa dubunnan mutane cikin halin ƙaka-ni-kayi da kuncin rayuwa yayin da suke neman mafaka a wasu wuraren da ake ganin suna da tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

