Juyin Mulki: Shugaba Bola Tinubu Ya Yi Kira ga Sojoji kan Dimokuradiyya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muhimmancin ladabi, biyayya da haɗin kai a cikin rundunonin soji, yana mai cewa su ne ginshiƙin ƙarfin ƙasa da dimokuraɗiyya
- Gwamnati ta sake tabbatar da kudurinta na inganta walwalar sojoji ta hanyar kayan aiki, horo da ingantaccen yanayin rayuwa domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa
- An kaddamar da sabbin shirye-shiryen ƙasa baki ɗaya domin girmama sojoji da ke bakin aiki da tsofaffin jarumai, tare da karrama wasu manyan hafsoshin dakarun Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga rundunonin sojin Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu tsayin daka kan ladabi, biyayya da haɗin kai.
Shugaban ya bayyana cewa rawar da sojoji ke takawa ta kunshi tabbatar da haɗin kan al’umma a Najeriya, ƙasa mai kabilu masu yawa.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Bola Tinubu ya isar da saƙon ne ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, a lokacin bikin tunawa da sojoji na shekarar 2026.
Kiran Bola Tinubu ga Rundunonin soji
Shugaba Tinubu ya ce a matsayinsa na babban kwamandan rundunonin soji, yana umartar dukkan jami’ai da sojoji da su ci gaba da riko da ƙa’idojin aikinsu.
Ya ce ladabi, biyayya da haɗin kai su ne ginshiƙan aikin soja, kuma dole ne a kiyaye su a kowane lokaci domin tabbatar da zaman lafiya.
Bola Tinubu ya kuma yi kira ga sojoji da su kasance masu biyayya ga Kundin Tsarin Mulki da dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa kare haɗin kan ƙasa yana da muhimmanci.
Shugaban ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa rundunonin soji domin su iya fuskantar ƙalubalen tsaro cikin ƙwarewa da jajircewa.
Maganar kula da walwalar sojoji
Tinubu ya bayyana cewa walwalar sojoji na da alaka da tsaron ƙasa, inda ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki don samar da ingantattun kayan aiki, ƙarin horo da kyautata yanayin rayuwa ga sojoji.
Vanguard ta rahoto ya ce gwamnatinsa za ta saka wa sojoji bisa sadaukarwar da suke yi da tallafi, domin ƙarfafa musu gwiwa a aikinsu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.

Source: Facebook
Shugaban ya kuma yaba da nasarorin da rundunonin soji suka samu a ayyukansu na baya-bayan nan, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen dawo da kwarin gwiwa da tsaro a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
A ƙarshe, an bayar da lambobin yabo ga wasu manyan jami’an soji da ke bakin aiki da kuma tsofaffi, ciki har da Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.
Yadda aka taimaki Tinubu a 2023
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya fadi rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarar Bola Tinubu a 2023.
Lai Mohammed ya bayyana cewa ya yi amfani da ofishinsa wajen tabbatar da jam'iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa a lokacin.
A bayanin da ya yi, tsohon ministan ya bayyana cewa 'yan adawa sun sako APC a lokacin da ake dab da zaben, amma dabarun da ya yi sun wargaza shirinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

