Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Kaduna, an Kashe Tsageru

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga a Kaduna, an Kashe Tsageru

  • Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindigan da suka addabi mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Kaduna
  • Jami'an tsaron sun kai samame a wata maboyar 'yan bindiga inda suka samu nasarar tura wasu daga cikinsu zuwa barzahu
  • Hakazalika, dakarun sojojin na rundunar Operation Enduring Peace sun samu nasarar kwato makamai da babura daga maboyar 'yan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji na rundunar hadin gwiwa ta Operation Enduring Peace, sun kai samame wata maboyar 'yan bindiga a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Sojojin sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin ’yan bindiga, tare da ceto wata mata da aka sace tare da kwato makamai, harsasai da babura.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kaduna
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke mutane 3 dauke da kayayyakin hada bama bamai a Daura

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ranar Talata, 13 ga watan Janairun 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan masu aikata laifuffuka da ke aiki a yankin.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Kaduna

A yayin samamen, an ce dakarun sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane hudu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da yiwuwar samun raunuka.

Abubuwan da aka kwato daga maboyar sun hada da bindiga guda da aka kera da hannu, harsasai biyar masu kaurin 7.62mm da kuma babura guda biyu.

Binciken farko ya nuna cewa mutanen da aka hallaka mambobi ne na wata kungiyar masu aikata laifuffuka da ke da alhakin kai hare-hare a kan hanyar Ganawuri–Manchok.

Dakarun Sojoji sun ceto wata mata

A wani lamari makamancin haka, dakarun sun gaggauta daukar mataki bayan samun bayanai kan sace wata matashiya mai suna Immaculate Samuel.

An sace matashiyar ne da daddare ranar 13 ga Janairu a kauyen Kajim, da ke a karamar hukumar Kaura.

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dakarun sun bi sawun masu garkuwar, lamarin da ya kai ga wata musayar wuta, inda aka hallaka wasu mutum uku daga cikin masu laifin, yayin da aka ceto wacce aka sace cikin koshin lafiya ba tare da samun rauni ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya magantu bayan Amurka ta kawo tallafin kayan aiki ga sojojin Najeriya

Daga bisani an yi wa wacce aka ceto tambayoyi na tsaro tare da mayar da ita hannun 'yan uwanta.

Jami’an tsaro sun ce dakarun na ci gaba da mamaye yankin domin bin diddigin sauran mambobin kungiyar masu aikata laifuffuka tare da kamo su, da kuma dawo da zaman lafiya a al’ummomin da abin ya shafa.

Wasu 'yan bindiga sun kashe soja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka soja da wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Benue.

'Yan bindigan sun aikata mummunan aikin ne a garin Udeku da ke gundumar Turan, ƙaramar hukumar Kwande ta jihar Benue.

2025 ta jefa mazauna yankin cikin fargaba, inda mutane da dama suka tsere daga gidajensu, yayin da al'amuran yau da kullum suka daina tafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng