Duk da Harin Amurka, ’Yan Sokoto Sun Fadi Yadda Barazanar Bello Turji Ke Tarwatsa Su

Duk da Harin Amurka, ’Yan Sokoto Sun Fadi Yadda Barazanar Bello Turji Ke Tarwatsa Su

  • Shugabanni da masu ruwa da tsaki a garuruwan dake gabashin jihar Sokoto sun yi ƙorafi kan barazanar hare-haren Bello Turji
  • Mutanen suna neman agajin gaggawa daga gwamnati da jami’an tsaro domin kawo karshen ta'addanci da ya addabe su
  • Fiye da ƙauyuka 20 suna tserewa, yayin da wasu mazauna suka tsallaka zuwa Jamhuriyar Nijar domin tsira daga barazanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Shugabanni da masu ruwa da tsaki daga mazabar Sokoto ta Gabas sun koka game da halin rashin tsaro da suke ciki.

Shugabannin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo ɗauki cikin gaggawa ga al’ummomin Tidibale da sauran yankuna da ayyukan Bello Turji suka tarwatsa a kwanakin nan.

Bello Turji na ci gaba da sheke ayarsa a Sokoto
Dan ta'adda Bello Turji da Ministan tsaro, Christopher Musa. Hoto: @HQNigerianArmy.
Source: Twitter

'Yan Sokoto sun koka da barazanar Bello Turji

Sakataren 'Sokoto Eastern Zone Development Association', Mu’azu Shamaki, shi ya tabbatar da haka ga wakilin Channels TV a ranar Laraba 14 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Yaran Turji sun yi ta'asa a Sokoto bayan sakon dan ta'addan ya rikita jama'a

Shamaki ya tabbatar da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda aka ga mutanen Tidibale na ficewa daga ƙauyukansu bayan barazanar Bello Turji, gaskiya ne, yana mai cewa lamarin ya jefa al’umma cikin mummunan hali da wahala mai tsanani.

Masu ruwa da tsakin sun bayyana damuwa kan barazanar hare-hare da Bello Turji da yaransa ke yi, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankunan da dama barin gidajensu domin tsira da rayuka.

Ya ce sama da ƙauyuka 20 ne abin ya shafa, inda ya ƙara da cewa mazauna yankin na fatan hukumomin tsaro za su tunkari ’yan ta’addan, domin su samu damar komawa gidajen kakanninsu.

Shi ma da yake tsokaci, Malam Bashar Guyawa-Isa ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa sun tsallaka zuwa wasu ƙauyuka a Jamhuriyar Nijar, suna neman mafaka saboda tsananin fargabar hare-hare.

Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa, yana mai cewa ƙauyuka da dama sun zama kufai, yayin da tsoro ya mamaye al’ummar sassan jihar sakamakon barazanar Bello Turji da mutanensa.

Mutane na tserewa daga Sokoto saboda Bello Turji
Taswirar jihar Sokoto na daga cikin jihohi da ke fama da matsalar ta'addanci. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda mutane ke tserewa daga gidajensu

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun tsere daga gidajensu, inda bayanai da ba a tabbatar da sahihancinsu ba ke nuna mazauna yankuna suna tserewa cikin motoci masu cike da jama’a fiye da kima, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Mutanen kauyuka za su kaura domin luguden wuta kan 'yan bindiga a dazuka

A wani ɓangare kuma, an samu rahotannin cewa ’yan bindiga na tserewa zuwa wasu sassan ƙasar, bayan da gwamnatin Amurka ta kai hare-hare ta sama kan sansanonin ’yan ta’adda a Sokoto a watan Disambar 2025.

Hakan ya na zuwa ne bayan gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa hare-haren da ta kai kan ƙungiyoyin ’yan jihadi a Arewa maso Yammacin Najeriya an yi su ne da amincewar Gwamnatin Najeriya.

Yaran Turji sun yi ta'asa a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa ’yan bindiga da ake danganta su da Bello Turji sun kai hari ƙauyen Gajit a Sabon Birni, inda suka jikkata mutane.

Wannan mummunan harin ya ƙara tayar da hankula kan ci gaba da ta’addancin Bello Turji da ƙungiyarsa a Gabashin Sokoto.

Jama’a na neman agajin gaggawa da tsari mai kyau na tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma masu rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.