Shugaban Kwamitin Harajin Tinubu na Tsaka Mai Wuya, An Fara Barazanar Tura Shi Lahira

Shugaban Kwamitin Harajin Tinubu na Tsaka Mai Wuya, An Fara Barazanar Tura Shi Lahira

  • Shugaban kwamitin gyara haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele ya ce rayuwarsa na fuskantar barazana saboda kokarin da yake yi
  • Oyedele ya ce an fara barazanar kashe shi saboda namijin kokarin da yake na gyara tsarin harajin Najeriya domin amfanin 'yan kasa
  • Ya ce har yanzu mutane da dama ba su fahimci manufar sababbin dokokin haraji ba, inda ya ce dokokin za su rage wa mutane kudin da suke biya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Kwamitin Gyara Fasalin Haraji na Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana hadarin da rayuwarsa ke fuskanta a yanzu.

Mista Taiwo Oyedele ya ce wasu mutane sun fara bazanar raba shi da duniya saboda rawar da ya taka wajen sauya dokokin haraji a Najeriya.

Shugaban kwamitin haraji, Taiwo Oyedele.
Shugaban kwamitin gyara tsarin haraji a Najeriya, Taiwo Oyedele Hoto: @Taiwooyedele
Source: Facebook

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Oyedele ya bayyana haka ne a ranar Talata a birnin Abuja, yayin wani taron bikin taya Hajiya Hadiza Bala Usman, murnar cika shekaru 50 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta hango matsala, ta bayyana abin da ke kara rura wutar matsalar tsaro a Najeriya

An fara barazana ga rayuwar Oyedele

Da yake jawabi a taron, Oyedele ya bayyana cewa aiwatar da sauye-sauye, musamman na haraji, abu ne mai matuƙar wahala domin yana shafar manyan masu ruwa da tsaki.

“Sauye-sauye abu ne mai wuya, amma sauya fasalin haraji ya fi wahala. Ana buƙatar ƙarfin zuciya. Ana mini barazana ne kawai saboda ƙoƙarina na gyara tsarin da ya lalace,” in ji shi.

Ya bayyana cewa suna fuskantar manyan ƙalubale wajen aiwatar da dokokin haraji, ciki har da rashin yarda da gwamnati, al’adar biyan haraji, da kuma rashin fahimta tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa.

A cewarsa, harajin da Najeriya ke tattarawa ya yi ƙasa ƙwarai idan aka kwatanta da sauran ƙasashe makamanta, abin da ya sa sauye-sauyen suka zama dole.

Oyedele ya buƙaci ’yan Najeriya da ke goyon bayan sauye-sauyen da su fito su bayyana ra’ayoyinsu, yana mai gargaɗin cewa shiru na bai wa masu adawa damar cin karensu babu babbaka.

Kara karanta wannan

"Ina ya shiga?" Peter Obi ya fito da damuwarsa game da yawan tafiye tafiyen Tinubu

Yaushe za a aiwatar da dokokin haraji?

Gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da sababbin dokokin haraji daga 1 ga Janairu, 2026, lamarin da ke ci gaba da fuskantar suka daga bangarori daban-daban na 'yan Najeriya.

Oyedele ya bayyana cewa rashin amana ita ce babbar matsalar da ke kawo cikas ga sauye-sauyen harajin da gwamnatin tarayya ta yi, in ji rahoton Channels tv.

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana duba takardu a ofishinsa a Aso Rock Villa Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Ya kuma ce akwai gibi wajen wayar da kai, inda wasu ’yan ƙasa ke tunanin an ƙara musu haraji, alhali gwamnati na ƙoƙarin ragewa da haɗa haraji daban-daban wuri guda.

“Ba zato aka wayi gari mutane na zagin gwamnati bisa zargin ta zo da haraji iri-iri, alhali abin da muka yi shi ne rage harajin da ake biya da kuma haɗa su wuri guda,” in ji shi.

Za a rika cirewa 'yan Najeriya haraji a banki?

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kwamitin haraji, Taiwo Oyedele ya musanta rade-radin cewa za a fara cire wa yan Najeriya kudi daga asusun bankuna.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi bayani game da sabon shirin Tinubu kan matsalar tsaro

Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan Najeriya na fargabar cewa za a rika cirar kudi a asusun ajiya na bankinsu domin biyan gwamnati kudin haraji.

Taiwo Oyedele ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sababbin dokokin ba za su janyo cire kudi kai tsaye daga asusun banki ba, komai girman kudin da aka tura.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262