Bayan Kwanaki, 'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Harin Amurka a Najeriya
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce tana da bayanai kan hare-haren jiragen yakin Amurka da aka kai a Sokoto, amma ba za ta bayyana su ga jama’a ba
- Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce batun ya shafi tsaro ne na kasa, don haka ya dace hukumomin tsaro na soja su yi bayani kai tsaye
- Legit Hausa ta rahoto cewa an kai hare-haren ne a ranar 25, Disamba, 2025, inda Amurka ta ce an kashe ‘yan ta’addar ISIS bisa bukatar gwamnatin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa tana da cikakken bayani game da hare-haren jiragen yakin Amurka da aka kai kan ‘yan ta’adda a jihar Sokoto, amma ba za ta fito ta bayyana bayanan ga jama’a ba.
A bayanin da ta yi, rundunar ta ce batun yana da nasaba da tsaron kasa, don haka ya dace a bar shi a hannun hukumomin tsaro na soja.

Source: Facebook
Wannan bayani ya fito ne daga bakin kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa, Benjamin Hundeyin, yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Television.
Ya ce rundunar ‘yan sanda na taka muhimmiyar rawa a fannin tattara bayanan sirri, amma ba dukkan bayanan tsaro ne ya dace a fitar da su fili ba.
Bayanin 'yan sanda kan harin Amurka
Da yake amsa tambaya kan ko rundunar ‘yan sanda ta san abin da ya faru a yayin harin, Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa:
“Aikin mu ne tattara bayanan sirri, ba wai fitar da bayanan sirri ba. A matsayinmu na rundunar ‘yan sanda, mun san wasu abubuwa game da wadannan hare-haren, amma ba ma son mu yi magana a kansu.”
Ya kara da cewa rundunar ta yanke shawarar kin yin tsokaci kai tsaye kan harin, yana mai jaddada cewa:
“Ba za mu yi magana kan wannan aiki na musamman ba.”
A cewar Benjamin Hundeyin, hakan ba yana nufin rundunar ba ta da masaniya ba ne, sai dai saboda muhimmancin batun tsaron kasa.
Hundeyin ya kuma bayyana cewa an samu hadin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban a yayin aiwatar da harin, amma ya ce ya fi dacewa rundunar tsaro ta yi bayani.
Harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren jiragen yakin Amurka sun faru ne a ranar 25, Disamba, 2025, a wasu yankuna na jihar Sokoto.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa hare-haren sun yi sanadin kashe ‘yan ta’addan ISIS da dama, tana mai cewa an kai su ne bisa bukatar gwamnatin Najeriya.

Source: Facebook
A cewar hukumomin Amurka, hare-haren sun kasance wani bangare na kokarin dakile ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke fakewa.
Sai dai hukumomin Najeriya da Amurka ba su fitar da cikakken bayani kan adadin wadanda abin ya shafa ba bayan kusan mako uku.
An ce harin Amurka ya kashe Lakurawa
A wani labarin, mun kawo muku cewa wani rahoto ya yi ikirarin cewa harin da sojojin Amurka suka kawo Najeriya ya kashe Lakurawa 155.
Rahoton da wata cibiya ta fitar ta ce harin ya kashe Lakurawa ne duk da cewa shugaban Amurka, Donald Trump cewa ya yi sun kashe 'yan ISIS.
An samu wasu masu bincike da suka bayyana cewa harin bai samu nasarar kashe 'yan ta'adda ba, sabanin sanarwar gwamnatin Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


