Yaran Turji Sun Yi Ta’asa a Sokoto bayan Sakon Dan Ta’addan Ya Rikita Jama’a
- ’Yan bindiga da ake danganta su da Bello Turji sun kai hari ƙauyen Gajit a Sabon Birni, inda suka jikkata mutane
- Harin ya ƙara tayar da hankula kan ci gaba da ta’addancin Bello Turji da ƙungiyarsa a Gabashin Sokoto
- Jama’a na neman agajin gaggawa da tsari mai kyau na tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma masu rauni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Al'mmar wasu yankuna a jihar Sokoto sun ga ta kansu bayan harin yan bindiga wanda ya yi sanadin raunata mutane biyu.
Ana zargin yaran Bello Turj ne suka kai hari yayin da wasu ke tserewa daga garuruwansu saboda zargin hare-hare.

Source: Twitter
Rahoton Bakatsine a shafin X ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata 13 ga watan Janairun 2026 a ƙauyen Gajit da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, a gundumar Lajinge ta Jihar Sokoto.
Yadda sakon Turji ya firgita al'mmar Sokoto
Harin na zuwa ne bayan wasu al'ummar jihar sun fara tserewa daga garuruwansu bayan samun sakon Bello Turji na kai musu hari.
Kasurgumin dan bindigar, Bello Turji ya turo sako mai daga hankali ga mazauna Tidibale a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen kauyen, wadanda galibinsu manoma ne sun fara guduwa daga gidajensu domin neman tsira.
Ana zargin Turji ya dauki wannan mataki ne domin nuna cewa har yanzu yana da karfin iko bayan tsawon lokaci da daina jin duriyarsa.

Source: Original
Yaran sun yi barna a wasu yankunan Sokoto
An ce ’yan bindiga da ake zargin suna biyayya ga shahararren jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji ne sukakai mummunan harin.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya yi sanadin raunata mutane biyu, yayin da aka yi garkuwa da akalla mutane 20, ciki har da maza da mata, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar hare-hare da kisan gilla da ake dangantawa da Bello Turji da ƙungiyarsa ta ’yan ta’adda, musamman a yankin Sokoto ta Gabas.
Biyo bayan wannan lamari, al’umma da masu ruwa da tsaki na nuna damuwa kan irin matakan tsaro na gaggawa da na dogon lokaci da gwamnati ke aiwatarwa domin dakile ta’addancin Bello Turji.
Mutanen yankin na kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi, su ɗauki matakai masu tsauri, tare da samar da tsaro mai ɗorewa domin kawo ƙarshen wannan ta’addanci da ke addabar al’ummar Sokoto ta Gabas.
Babu gaskiya kan jita-jitar kisan Turji
A baya, kun ji cewa a ranar Lahadi 28 ga watan Disambar 2025 aka yada rade-radin harin Amurka da aka kai a Sokoto ya yi ajalin Bello Turji.
Amurka dai ta kai harin ne a ranar Kirsimeti kan wasu yan ta'adda da ta kira da yan kungiyar ISIS a wasu yankuna.
Masu bincike sun ce labarin kisan Turji ya samo asali ne daga bayanan bogi da suka dade da aka sake yadawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

