Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya Ta Biya Kamfanin Amurka $9bn don Gyara Alaka da Trump
- Gwamnatin tarayya ta dauki wani kamfanin Amurka a kan kwangilar $9m domin yin kamun ƙafa a madadin gwamnatin Najeriya ga Donald Trump
- Aster Legal daga Kaduna ce ta dauki DCI Group a madadin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa, Nuhu Ribadu domin mika bayanan kare Kiristoci ga Amurka
- An dauki matakin ne yayin da Amurka ke haƙiƙancewa a kan zargin ana kashe kiristoci a Najeriya tare da yi wa ƙasar barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin tarayya ta dauki wani kamfanin kamun ƙafa a Amurka da kwangilar $9m domin taimaka mata wajen isar da bayanai ga gwamnatin Amurka kan matakan kare Kiristoci a kasar.
Takardun kwangilar da aka mika wa Ma’aikatar Shari’a ta Amurka sun nuna cewa kamfanin Aster Legal da ke jihar Kaduna ne ya dauki DCI Group a madadin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa Nuhu Ribadu.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa DCI Group kamfani ne na hulda da jama’a da kamun kafar siyasa da ke Amurka.
Najeriya ta dauki kamfanin kamun kafar Amurka aiki
Politics Nigeria ta ruwaito cewa takardar yarjejeniyar ta nuna cewa Oyetunji Olalekan Teslim, babban abokin hulda na Aster Legal, da Justin Peterson, babban daraktan DCI Group, ne suka sanya wa yarjejeniyar hannu a ranar 17 ga Disamba, 2025.
Bisa ga bayanan da ke cikin kwangilar, DCI Group za ta taimaka wa gwamnatin Najeriya ta hannun Aster Legal wajen isar da bayanai kan matakan kare Kiristoci.
Haka kuma ana sa ran kamfanin zai yi kamun kafa a madadin Najeriya domin ci gaba da samun goyon bayan Amurka wajen yakar kungiyoyin ta'adda.
An amince kwangilar za ta fara aiki na tsawon watanni shida zuwa 30 ga Yuni, 2026, kuma za a sabunta ta kai tsaye na wasu watanni shida idan buƙata ba ta biya ba.
Haka kuma, kwangilar ta tanadi damar da kowane bangare zai iya dakatar da ita a kowane lokaci ba tare da wata tara ba, muddin an ba da sanarwa a rubuce kwanaki 60 kafin ranar dakatarwa.
A ranar 12 ga Disamba, Najeriya ta biya DCI Group Dala miliyan 4.5 a matsayin kudin watanni shidan farko na wannan yarjejeniya.
Wani sashe na kwangilar ya ce:
"Abokin huldar zai rika biyan mai ba da shawara Dala dubu 750,000 a kowane wata a matsayin cikakken kudin aiki. Za a biya kudin ne kashi biyu na watanni shida – na farko a lokacin sanya hannu, na biyu kuma bayan cikar watanni shida.
Dalilin daukar kamfanin da martanin Amurka
Gwamnatin tarayya ta dauki matakin daukar kamfanin ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka ke nuna sha’awa da damuwa kan rahotannin kashe-kashen Kiristoci a Najeriya.
A watan Oktoba, shugaban Amurka Donald Trump ya sake ayyana Najeriya a matsayin kasa da ake da damuwa a kanta, bisa zargin ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi.
Gwamnatin Najeriya ta sha musanta zargin, tana mai cewa babu kisan kiyashi na addini, tare da alkawarin tattaunawa da Amurka domin a fahimci juna.

Kara karanta wannan
Shehu Sani ya magantu bayan Amurka ta kawo tallafin kayan aiki ga sojojin Najeriya

Source: Getty Images
A watan Nuwamba, Trump ya yi barazanar cewa zai shiga Najeriya da karfi domin murkushe ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci, bayan wasu ‘yan siyasar Amurka sun yi ikirarin ana kisan kiyashi kasar.
A ranar Kirsimeti, Amurka ta kai hare-haren sama kan wasu sansanonin ‘yan ta’adda biyu a dajin Bauni da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, abin da ya kara janyo hankalin kasashen waje kan batun tsaro a Najeriya.
Amurka ta kawo kayan yaki Najeriya
A baya, kun ji cewa Amurka ta kai muhimman kayan aikin sojoji ga hukumomin tsaron Najeriya a wani mataki da ke nuna ci gaba da goyon baya wajen yaƙi da ta’addanci.
Wannan tallafi ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar, musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Jirgin da ya kawo kayan aikin ya sauka ne a Abuja, babban birnin tarayya, inda aka mika kayan ga hukumomin tsaro da abin ya shafa. An dauki hoton jirgin tare da kayan aikin.
Asali: Legit.ng

