Matar Aure Ta Mutu bayan Barin Almakashi a Cikinta Yayin Tiyata a Kano

Matar Aure Ta Mutu bayan Barin Almakashi a Cikinta Yayin Tiyata a Kano

  • Wani mazaunin Kano ya zargi asibitin Abubakar Imam Urology da sakaci a aikin jinya bayan mutuwar matarsa sakamakon tiyata da aka mata
  • Mijinta ya ce an yi mata tiyata ne a watan Satumba, amma daga bisani ta rika fama da tsananin ciwon ciki ba tare da cikakken bincike ba
  • Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta bayar da umarnin bincike mai zurfi kan zargin da aka gabatar na cewa an bar almakashi a cikin matar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Wani mazaunin birnin Kano, Abubakar Muhammad, ya bayyana yadda matarsa, Aishatu Umar, ta rasu bayan wasu matsaloli da suka biyo bayan tiyatar da aka yi mata a Abubakar Imam Urology.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: DSS tana binciken zargin samun makamai a gidan Malami

Muhammad ya zargi asibitin da sakaci a aikin jinya, yana mai cewa an bar almakashi a cikin cikinta bayan an yi mata tiyata, lamarin da ya janyo ciwon da ya addabe ta tsawon watanni kafin rasuwarta.

Aisha Umar da ta rasu bayan barin almakashi a cikinta
A hagu, marigayiya Aisha Umar, a dama kuma hoton almakashin da aka dauka a cikinta Hoto: AbdulRazaq Dahiru Kaita
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a Kano, inda Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta ce za ta gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Halin da matar ta shiga bayan tiyata

Abubakar Muhammad ya ce matarsa ta kamu da rashin lafiya watanni da suka gabata, kuma daga bisani aka yi mata tiyata a asibitin. A cewarsa, bayan an sallame ta daga asibitin, ta fara fama da tsananin ciwon ciki da bai gushe ba.

Ya ce duk lokacin da take komawa asibitin domin kai korafi, ma’aikatan lafiya kan ba ta magungunan rage radadi kawai, ba tare da yin wani zurfin bincike ba. A cewarsa, ana sha gaya mata cewa irin wannan ciwo abu ne na yau da kullum ga masu tiyata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Muhammad ya nuna damuwa kan yadda ba a taba ba da shawarar yin hoton x-ray ko wani bincike na zamani domin gano musabbabin ciwon ba, duk da cewa yana ta tsananta.

An bar almakashi a cikin mata bayan tiyata

A cewar mijin marigayiyar, bayan kusan wata hudu na fama da radadi, suka kai korafi wasu asibitoci domin yin cikakken gwaji.

A nan ne aka gudanar da gwaje-gwaje da na’urorin bincike a Muhammad Abdullahi Wase Specialist Hospital da kuma Aminu Kano Teaching Hospital.

Sakamakon gwaje-gwajen, kamar yadda Muhammad ya bayyana, ya nuna cewa an bar almakashi na tiyata a cikin cikinta tun daga aikin da aka yi mata.

An fara shirye-shiryen yi mata wata tiyata domin cire abin da aka bari a jikinta, amma kafin a kai ga aiwatar da hakan, Aishatu Umar ta rasu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An bude sabon bincike bayan gano bindigogi da alburusai a gidan Malami

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A martaninta, Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta bayar da umarnin gudanar da bincike nan take domin gano gaskiyar abin da aka ce ya faru.

Ana jimamin mutuwar sarki a Legas

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban karamar hukumar Badagry a jihar Legas ya sanar da cewa za a shafe kwana 7 ana jimamin mutuwar sarkinsu.

Mai martaba Aholu Menu Toyi I na Badagry ya rasu ne bayan shafe kusan shekara 50 ana kan mulki, lamarin da ya girgiza jama'ar yankin.

Sanarwar da shugaban karamar hukumar ya fitar ta nuna cewa an samu sahalewar gwamna Babajide Sanwo-Olu kafin ayyana kwanakin zaman makokin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng