Gwamna Ya Faɗi Waɗanda Suka Ɗauki Nauyin Zanga Zanga, Hari kan Hausawa
- Gwamna Monday Okpebholo, ya yi magana game da zanga-zanga da ta barke a jihar Edo a ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2026
- Gwamnan ya ce abin da ya faru na tarzoma a Ekpoma ba zanga-zangar dalibai ba ce, illa rikici da aka shirya kuma aka dauki nauyinsa
- Okpebholo ya ce jami’an tsaro sun gano wani dan Najeriya mazaunin Rasha da wasu a kasashen waje da ake zargi suna daukar nauyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Gwamna Monday Okpebholo, ya nuna bakin cikinsa game da zanga-zangar da ta barke a jihar Edo.
Okpebholo ya bayyana cewa an gano masu daukar nauyin zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma a Ekpoma.

Source: Twitter
Zanga-zangar Edo: Ana zargin hannun wasu a ketare
Gwamnan ya ce abin da ya faru ba zanga-zangar dalibai ba ce, illa tsararren rikici da aka ɗauki nauyi, cewar The Nation.
Okpebholo ya wani dan Najeriya mazaunin Rasha ne da wasu a kasashen waje suka dauki nauyinsa.
A cewar Okpebholo, akwai manyan alamomi da ke nuna cewa ‘yan adawa, watakila da goyon bayan kasashen waje, suna daukar nauyin tayar da hankula.
Ya ce manufar hakan ita ce bata sunan gwamnatin Edo da kuma haddasa rikici domin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Patrick Ebojele, ya fitar a madadin gwamnatin jihar.
An gano masu kitsa rigima a Edo
Rahoton ya kara da cewa jami’an tsaro sun gano shugabannin rikicin da suka tuntubi mutane a Ekpoma domin shirya tarzoma.
Sanarwar ta ce an shirya fadada rikicin zuwa Auchi, Irrua har ma da fadar gwamnatin jihar da ke Benin City, da kudade daga kasashen waje.
A cewar sanarwar, wasu daga cikin wadanda aka kama an tare su ne yayin da suke kan hanyarsu ta lalata dukiyoyi a harabar jami’a.
Sauran kuma an gano fuskokinsu ne a cikin wani bidiyo da ya yadu, wanda ya nuna kone-kone da lalata dukiyoyi yayin tarzomar.

Source: Original
Dalilin kama Masu zanga-zanga a Edo
Gwamnatin ta ce galibin kama mutanen ya ta’allaka ne kan hujjoji karara, ciki har da bidiyon da ke nuna tashin hankali da barna, cewar Punch.
Ta jaddada cewa wadanda aka kama masu ta da tarzoma ne, ba masu zanga-zangar lumana ba kamar yadda wasu ke kokarin nunawa.
Okpebholo ya tabbatar wa mazauna Ekpoma cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin, kuma zaman lafiya na ci gaba da dawowa.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da bidiyoyin bogi da rahotannin da ba a tantance ba, tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali.
An kai hari kan Hausawa a Edo
Mun ba ku labarin cewa fusatattun matasa sun kori Hausawa a kasuwar dabbobi ta Ekpoma, inda suka yanka awaki sakamakon zanga-zanga.
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kira da a kwantar da hankali domin kauce wa ramuwar gayya.
Yan sanda sun ce an ceto mutane tara da aka sace bayan amfani da na’ura inda aka tilasta masu garkuwa tserewa.
Asali: Legit.ng

