Magana Ta Girma: DSS Tana Binciken Zargin Samun Makamai a Gidan Malami
- Hukumar DSS ta fara bincike kan tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, bayan rahoton gano makamai a gidansa
- Rahoto ya ce EFCC ce ta gano makaman yayin binciken zargin cin hanci, amma ta mika su DSS saboda bin doka
- Duk da samun beli kan shari’ar N8.7bn, Malami na ci gaba da zama a gidan gyaran hali, yayin da ake zargin yana gujewa sake kamawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta fara sabon bincike kan tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami.
Majiyoyi sun ce ana zargin an gano makamai da alburusai a gidansa da ke Birnin Kebbi a jihar Kebbi.

Source: Facebook
EFCC ta samu makamai a gidan Abubakar Malami
Jaridar The Nation ce ta fara wallafa labarin, inda ta ce ta samu bayanai daga majiyoyin tsaro da ke da masaniya kan lamarin da ke gudana.
Rahoton ya bayyana cewa jami’an Hukumar EFCC sun gano makaman ne yayin da suke binciken gidan Malami a cikin binciken zargin laifukan kudi da ake yi masa.
Sai dai saboda mallakar makamai ba ta cikin hurumin EFCC, an ce hukumar ta mika dukkan makaman da aka gano ga DSS domin ci gaba da bincike.
Majiyoyi sun bayyana cewa har yanzu ba a tantance adadin da irin makaman ba, amma sun ce sun isa su sa a kaddamar da cikakken bincike daga DSS.
Malami, wanda ya rike mukamin Antoni-Janar daga 2015 zuwa 2023, ya samu beli makon da ya gabata tare da matarsa da dansa kan shari’ar safarar kudi ta N8.7bn.
Duk da hukuncin beli, Malami na ci gaba da zama a gidan gyaran hali na Kuje, saboda har yanzu bai cika sharuddan belin ba.

Source: Facebook
Zargin da ake yi wa Malami kan beli
Sahara Reporters ta ruwaito cewa Malami na jinkirta cika belin ne domin kauce wa sake kama shi da DSS ke shirin yi kan batun makamai da kuma zargin daukar nauyin ta’addanci.
Rahoton ya ce jami’an DSS da dama sun kewaye gidan gyaran hali na Kuje domin tabbatar da cewa Malami zai kasance a hannu idan aka sake shi.
Wata majiya ta tsaro ta ce jerin makaman da aka gano tuni sun shiga hannun DSS, inda ta ce:
“Yanzu Malami ne zai yin bayanin yadda ya mallaki makaman.”
Wata majiya daga hukumar EFCC ta tabbatar da cewa Malami bai kammala sharuddan belinsa ba, tana karyata jita-jitar da ke cewa an sake shi, cewar Premium Times.
EFCC ta kwace kadarorin Malami 57
Kun ji cewa wata babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da umarnin wucin gadi na kwace wasu kadarori da ake zargin na Abubakar Malami ne.
Mai shari'a Emeka Nwite ya ba da wa'adin kwanaki 14 ga duk wanda ke da hujjar mallakar dukiyoyin kafin kwace kadarorin gaba daya.
Wannan na zuwa ke bayan kotun ta ba da belin Malami da sauran wadanda ake tuhuma kan Naira biliyan 1.5 da sharudda masu tsauri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

