Kotu Ta Jiƙawa PDP Aiki, Ta Soke Zaɓen Fitar Gwani da Aka Yi na Gwamna a Ekiti

Kotu Ta Jiƙawa PDP Aiki, Ta Soke Zaɓen Fitar Gwani da Aka Yi na Gwamna a Ekiti

  • Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Ado-Ekiti ta soke zaben fitar da gwani na gwamnan PDP a zaben Ekiti a 2026 da ake shirin yi
  • A hukuncin da aka yanke, kotun ta kuma ba da umarni ga jam’iyyar ta sake shirya sabon zabe domin fitar da wani dan takarar gwamna
  • Alkali ya ce PDP ta karya dokoki saboda rashin gabatar da sahihin jerin wakilai, abin da ya sa aka ayyana zaben a matsayin mara inganci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Wata Kotun Tarayya da ke zamanta a babban birnin Ado-Ekiti jikawa PDP aiki bayan soke zaben fitar da gwani da ta yi.

Kotun ta soke zaben fitar da gwanin gwamnan jam’iyyar PDP mai adawa a jihar da ya haifar da tsaida Dr. Wole Oluyede.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kashe Naira biliyan 40 a zamanantar da gadar Legas da CCTV

Kotu ta soke zaben fitar da gwani da aka yi na PDP
Shugaban PDP a Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki yana jawabi bayan an zabe shi jagoran jam'iyyar. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Source: Facebook

Umarnin da kotu ta ba PDP a Ekiti

Kotun ta bayar da wannan hukunci ne a yau Talata 13 ga watan Janairun 2026 inda ta umurci jam’iyyar PDP ta gudanar da sabon zaben fidda gwamna a jihar, cewar rahoton Vanguard.

An yanke hukuncin ne yayin sauraron karar da wani dan takarar gwamna, Funsho Ayeni, ya shigar kan PDP da INEC.

Ayeni ya shigar da kara yana kalubalantar sahihancin zaben, yana zargin jam’iyyar da rashin gabatar da sahihin jerin wakilan zaben.

Ya ce rashin gabatar da asalin jerin wakilan doka da na wucin gadi ya sabawa ka’idojin PDP da kuma dokar zabe ta kasa.

Abin da alkalin kotun ya ce

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Mai shari’a Babs Kuewumi, ya ce zaben bai bi tanadin doka da kundin tsarin PDP ba.

Alkalin ya soke zaben fitar da dan takarar gwamnan tare da umartar PDP da hukumar INEC su shirya sabon zabe bisa doka da ka’idoji.

Kara karanta wannan

A karon farko, Fubara ya yi magana ga al'ummar Rivers game da shirin tsige shi

Kotun ta umurci a bai wa dukkan ‘yan takara masu cancanta damar shiga sabon zaben domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Mai shari’a Kuewumi ya ce wannan mataki zai karfafa dimokuradiyya da adalci a cikin jam’iyyar PDP, Channels TV ta ruwaito.

Tun da farko, kotun ta dage sauraron karar da aka shigar kan Oluyede zuwa ranar 8 ga Disamba, 2025.

Kotu ta rushe zaben fitar da gwani na PDP da aka yi
Taswirar jihar Ekiti da ake shirin gudanar da zabe gwamna a 2026. Hoto: Legit.
Source: Original

Ekiti: Wa ya lashe zaben fitar da gwani?

Rahotanni sun nuna cewa Wole Oluyede ya lashe zaben fidda gwamnan PDP da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

A wancan zaben, Oluyede ya samu kuri’u 279, inda ya doke Funsho Ayeni da kuma Funmi Ogun.

Kwamitin zaben da Sanata Ibrahim Dankwambo ya jagoranta ne ya gudanar da zaben fitar da gwani na takarar gwamna a inuwar PDP.

A karar mai lamba FHC/AD/CS/29/2025, Ayeni ya kalubalanci nasarar Oluyede a zaben tsaida 'dan takaran jam’iyyar.

Lauyan Ayeni, Kola Kolade SAN, ne ya jagoranci tawagar lauyoyi, yayin da manyan lauyoyi suka kare Oluyede da PDP.

PDP ta shiga matsala kan zaben 2026

Kara karanta wannan

An cafke jami’in DSS da ake zargi ya tursasa wa budurwa barin Musulunci bayan dirka mata ciki

An ji cewa Hukumar INEC da jam'iyyun siyasa na ci gaba da shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda za a gudanar a watan Yunin 2026.

Rahoto ya tabbatar da cewa INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takara 12 da mataimakansu, wadanda za su fafata a zaben.

Sai dai abin da ya ja hankali shi ne rashin ganin sunan dan takarar gwamnan PDP da mataimakinsa, wanda ake ganin yana da alaka da rikicin jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.