Amurka Ta Kawo Kayan Aiki ga Sojojin Najeriya Kwanaki bayan Farmakar 'Yan Ta'adda
- Amurka ta dauki mataki na gaba wajen ba Najeriya taimako a yakin da take yi da 'yan ta'adda da ayyukan ta'addanci
- Jirgin sama dauke da kayan aiki na sojoji ya iso birnin tarayya Abuja a matsayin tallafi daga kasar Amurka zuwa ga Najeriya
- A baya kasar ta kawo farmaki a jihar Sokoto kan 'yan ta'adda yayin da take da ci gaba da hadin gwiwa da Najeriya ta fuskar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kasar Amurka ta kawo kayan aiki na sojoji ga hukumomin tsaron Najeriya inda aka shafe shekara da shekaru ana yaki da ta'addanci.
Amurka ta kawo kayan aikin ne domin tallafa wa ayyukan tsaro da ake ci gaba da gudanarwa a kasar nan.

Source: Twitter
Rundunar Sojojin Amurka da ke kula da Afirka (AFRICOM) ce ta sanar da hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X (wadda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Talata, 13 ga watan Janairun 2026.
Kasar Amurka ta ba Najeriya tallafi
A cewar AFRICOM:
“Sojojin Amurka sun kai muhimman kayan aikin sojoji ga abokan hulɗarmu na Najeriya a Abuja. Wannan tallafi yana goyon bayan ayyukan tsaro da Najeriya ke gudanarwa tare da jaddada haɗin gwiwarmu ta tsaro.”
Sanarwar da aka wallafa, ba ta bayyana takamaiman irin kayan aikin sojan da aka kawo ba, haka kuma ba a faɗi adadinsu ba.
Wannan na zuwa ne yayin da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ke kara karfi.
Yadda Amurka ta kawo hari Najeriya
A daren ranar Kirsimeti, sojojin Amurka sun kai hare-haren sama a jihar Sokoto, inda suka kai farmaki kan ‘yan ta’addan da ke da alaƙa da kungiyar ISIS, waɗanda ake zargi da aiki tare da kungiyar Lakurawa da kuma wasu kungiyoyin ‘yan bindiga na cikin gida.
Hare-haren sun biyo bayan saɓanin diflomasiyya da ya taso sakamakon zargin cin zarafi da muzgunawa da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya
A baya, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana lamarin a matsayin “kisan kare dangi”, kalaman da gwamnatin Najeriya ta yi watsi da su.
Trump ya kuma soki Najeriya, yana kiran ƙasar da suna “wulakantacciya”, tare da barazanar ɗaukar matakin soja idan har gwamnati ta ci gaba da, a cewarsa, bari ana kashe Kiristoci.
Meyasa Amurka ta kawo kayan sojoji?
Rundunar AFRICOM ta bayyana cewa isar da kayan aikin sojan na da nufin karfafa sojojin Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci da sauran ayyukan tsaro
Ta ce kawo kayan aikin wani ɓangare ne na babbar dabarar Amurka ta karfafa haɗin gwiwar aiki da kasashen yankin Yammacin Afirka.

Source: Facebook
Najeriya dai ta shafe shekaru tana fuskantar hare-hare masu yawa daga kungiyoyin ‘yan bindiga da na ta’addanci a sassa daban-daban na kasar.
Har zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da wannan sabon tallafin da Amurka ta bayar.
Hare-haren Amurka sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa hare-haren da sojojin Amurka suka kawo a Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda.
Wani rahoto da aka fitar ya yi ikirarin cewa harin Amurka a Najeriya ya yi nasara tare da fadin adadin 'yan ta'addan Lakurawa da aka kashe.
Harin farko ya kashe kimanin ‘yan ta’adda 30, sannan bayan sauran suka taru domin taimaka wa waɗanda suka jikkata, aka sake kai hari na biyu wanda ya hallaka yawancinsu.
Asali: Legit.ng

