'Yan Bindiga Sun Mamayi Jami'an Tsaro, Sun Kashe Tsohon Dan Takarar Majalisa da Mutum 4

'Yan Bindiga Sun Mamayi Jami'an Tsaro, Sun Kashe Tsohon Dan Takarar Majalisa da Mutum 4

  • 'Yan bindiga sun kashe mutane biyar a wani kazamin hari da suka kai kauyen Otobi da ke Karamar Hukumar Otukpo a jihar Benuwai
  • Daga cikin mutanen da maharan suka kashe da karfe 1:30 ja safiyar yau Talata akwai tsohon dan takarar kujerar Majalisar dokokin jihar
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kai harin, amma ta ce mutane hudu ne suka rasa rayukansu ba mutum har biyar da aka fi yadawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue, Nigeria - Akalla mutane biyar, ciki har da tsohon dan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Benuwai na jam’iyyar PDP daga mazabar Otukpo-Akpa, Igbabe Ochi, sun rasa rayukansu a safiyar Talata.

Bayanai sun nuna cewa dan siyasar da wasu mutum hudu sun mutu ne lokacin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Otobi da ke Karamar Hukumar Otukpo a Jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

Sakon da Bello Turji ya aiko ya hargitsa mutane, an fara guduwa a jihar Sakkwato

Jihar Benue.
Taswirar jihar Benuwai da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hare-hare sun karu a yankunan Benuwai

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na dare, kwanaki biyu kacal bayan da jami’an tsaron sa-kai sun dakile yunkurin sace mutane a yankin Ekwu-Ora Odaba na Otobi.

Mazauna yankin sun ce Otobi na ci gaba da fuskantar hare-hare daga ’yan bindiga da ake zargin wasu fulani makiyaya ne, musamman wani mummunan hari da aka kai ranar 15 ga Afrilu, 2025, inda aka kashe mutum 13.

Haka kuma, a watan Mayun 2025, 'yan bindiga sun sake kashe wasu mutum uku a yankin, kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito.

'Yan bindiga sun mamayi 'yan sa-kai

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an sa-kai da matasa sun shafe daren Litinin suna sintiri har zuwa tsakar dare, amma bayan sun koma hutawa ne ’yan bindigar suka shiga garin.

“Lokacin da yan sa-kai a yankin layin dogo zuwa bangaren Ijami suka janye da misalin karfe 1:30 na dare, sai ’yan bindigan suka shiga garin suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ci gaba da ta'asa a Benue, an hallaka dan sanda da jikkata matafiya

“Sun kashe mutane biyar, sannan suka yi awon gaba da kayan abinci da sauran dukiyoyi,” in ji shi.
Jami'an yan sanda.
Dakarun rundunar yan sanda cikin shirin ko ta-kwana a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Rundunar 'yan sanda ya fadi abin da ya faru

A nasa bangaren, kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Benuwai, DSP Udeme Edet, ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce adadin wadanda suka mutu mutum hudu ne, ba biyar ba.

“Mun samu labarin cewa an kai hari a Otobi-Akpa da safiyar yau, inda abin takaici mutane hudu suka rasa rayukansu."
“Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalai da ’yan uwansu, yanzu haka muna ci gaba da bincike, kuma ana kokarin cafke wadanda suka aikata wannan mummunan laifi domin su fuskanci hukunci,” in ji ta.

'Yan bindiga sun farmaki matafiya a Benuwai

A wani rahoton, kun ji cewa ’yan bindiga sun kai hari kan motar bas mai jigilar fasinjoji ta kamfanin Benue Links a kan hanyar Makurdi–Otukpo.

Harin ya auku ne lokacin da wata motar Toyota Hiace mallakin kamfanin Benue Links Ltd, mai lambar rijista BUU 429 XB (Plateau), ta fada tarkon yan bindigar.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bude wa motar wuta ba zato ba tsammani, wanda hakan ya jikkata matafiya da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262