Matar Tsohon Gwamna a Najeriya Ta Rasu Tana da Shekaru 100 a Duniya
- An shiga jimami a jihar Ogun bayan tafka babban rashin matar tsohon gwamna da aka yi wanda ya tayar da hankula
- Uwargidan tsohon gwamnan farar hula na farko a Jihar Ogun, Lucia Onabanjo, ta rasu tana da shekaru 100 a ban kasa
- ’Yarta, Olubukunola Onabanjo, ta ce Lucia ta rasu cikin aminci bayan doguwar rayuwa mai albarka da ta yi a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ogun - Uwargidan tsohon gwamnan farar hula na farko a Jihar Ogun, Cif Olabisi Onabanjo ta rasu bayan fama da dohuwar jinya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa marigayiya Lucia Onabanjo ta rasu tana da shekaru 100 a duniya.

Source: Original
An sanar da rasuwar matar tsohon gwamna
’Yarta, Olubukunola Onabanjo, ce ta sanar da rasuwar mahaifiyarsu a cikin wata sanarwa da Punch ta samu da ta fitar ranar Talata 13 ga watan Janairun 2026.
A cewar sanarwar, Lucia, wacce ake ɗaukarta a matsayin uwar gida kuma ginshiƙin iyalan Onabanjo, ta rasu cikin aminci a ranar Litinin 12 ga watan Janairun 2026.
Wani ɓangare na sanarwar ya ce:
“Iyalin Cif Victor Olabisi Onabanjo, tsohon Gwamnan Jihar Ogun, na sanar da rasuwar mahaifiyarmu, kakarmu da kakar kakanni, cikin alhini mai zurfi amma tare da godiya ga Allah.
Lucia Onabowale Onabanjo (1925–2026) ta koma ga Mahaliccinta a ranar Litinin, 11 ga Janairun 2026 da muke ciki.”
Iyalin sun bayyana godiyarsu ga Allah bisa tsawon rayuwar da ta yi da kuma kyawawan halaye da ta bari, juriyya da nuna gaskiya yayin da take raye.
Sun kuma roƙi Allah ya gafarta mata, ya sanya ta cikin Aljanna Firdausi, tare da ba iyalai da masoya ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

Source: Twitter
Shekarun da mijin marigayiywar ya yi a mulki
Marigayi mijinta, Cif Olabisi Onabanjo, shi ne gwamnan farar hula na farko da ya jagoranci Jihar Ogun daga shekarar 1979 zuwa 1983.
Baya ga siyasa, Cif Onabanjo shahararren ɗan jarida ne, wanda aka fi sani da rubutun makalarsa ta mako-mako mai suna “Ayekooto”, wadda ta yi tasiri sosai a harkar jarida kafin rasuwarsa a shekarar 1990.
Rasuwar Lucia Onabanjo ta janyo alhini da jimami daga ’yan uwa, abokai da al’ummar Jihar Ogun, inda da dama ke yabon gudunmawar da ta bayar a rayuwarta ta iyali da zamantakewa.
Abin da gwamnatin Ogun ta ce
Gwamna Dapo Abiodun ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar tare da yi mata addu'a fatan samun rahama.
Abiodun ya bayyana rashin dattijuwar a matsayin abin takaici wacce zai yi wahala a iya maye gurbinta, kamar yadda Premium Times.
Matar marigayi Shehu Shagari ta rasu
A baya, kun ji cewa matar marigayi tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari, Hajiya Sutura ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a jihar Sokoto.
Hajiya Sutura, wacce ita kadai ta rage daga cikin matan marigayi Shehu Shagari ta rasu a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamba, 2025.
Iyalan Shagari sun tabbatar da wannan rashi, inda suka bayyana marigayiyar da uwa ta gari mai tawali'u, kulawa da kuma karamci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

