'Yan Bindiga Sun Ci Gaba da Ta'asa a Benue, An Hallaka Dan Sanda da Jikkata Matafiya

'Yan Bindiga Sun Ci Gaba da Ta'asa a Benue, An Hallaka Dan Sanda da Jikkata Matafiya

  • 'Yan bindiga sun kai hare-hare kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba lokacin da suke tsaka da tafiya a jihar Benue
  • Tsagerun sun jikkata matafiya bayan sun farmaki motar da ke dauke da su suna cikin tafiya a tsakiyar daji
  • Hakazalika, 'yan bindiga sun bude wuta ga wani jami'in dan sanda lokacin da yake tafiya tare da dan uwansa a cikin mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kan motar bas mai jigilar fasinjoji ta kamfanin Benue Links a kan hanyar Makurdi–Otukpo, inda suka jikkata mutum uku.

A wani hari daban da ya faru daga baya, an kashe wani jami’in ’yan sanda a karamar hukumar Otukpo ta jihar Benue.

'Yan bindiga sun kashe dan sanda a Benue
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Ba mu yadda da su ba": Amotekun ta tare mota ɗauke da Hausawa a hanyar Ondo

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Benue

Majiyoyi sun bayyana cewa harin farko ya faru ne da misalin karfe 7:20 na yamma ranar 10 ga Janairun 2026.

Harin ya auku ne lokacin da wata motar Toyota Hiace mallakin kamfanin Benue Links Ltd, mai lambar rijista BUU 429 XB (Plateau), ta fada tarkon kwanton bauna kusa da wani kamfanin bulo a kan hanyar Makurdi–Otukpo.

Motar bas ɗin, wadda ke kan hanyarta daga Gboko zuwa Legas, ta fuskanci harin ne daga ’yan bindigan da suka fito daga cikin daji suka bude wuta.

Rahotanni sun ce direban ya ci gaba da tukawa ba tare da tsayawa ba, duk da harbin bindiga da ake yi.

Sakamakon harin, fasinjoji uku Solomon Abbas, Stephen Aondoakaa da Justina Gosolo sun samu raunukan harbin bindiga.

Jami'an tsaron Benue sun kai dauki

An ce DPO na Otukpo ya gaggauta tura jami’an sintiri zuwa wajen, yayin da aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar kimiyyar lafiya ta tarayya, Otukpo, inda suke karbar magani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki amarya da wasu 'yan gidan biki, an rasa rayukan bayin Allah

Jami’an tsaro sun ci gaba da kewaye dazuzzukan da ke kusa domin bibiyar maharan.

'Yan bindiga sun kashe 'dan sanda

A wani lamari makamancin hakan, ’yan bindiga sun kashe wani jami’in ’yan sanda a kan hanyar Otobi kusa da Makarantar Ebenezer International a yankin Oko Otobi na karamar hukumar Otukpo.

Majiyoyi sun ce an kai rahoton lamarin ne da misalin karfe 6:45 na yamma ranar 11 ga Janairu, inda wani mutum ya bayyana cewa 'yan bindiga sun farmake su lokacin da yake tafiya ne tare da babban dan uwansa, ASP Godwin O. Otse.

Ya ce 'yan bindigan sun farmake su ne lokacin da suke tsaka da tafiya cikin motarsu kirar Honda Accord mai launin toka da misalin karfe 5:45 na yamma.

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda a Benue
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Maharan, da aka ce suna sanye da kayan sojoji, sun bude wuta kan motar, inda suka ji wa ASP Otse mummunan rauni.

An garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar kimiyyar lafiya ta tarayya, Otukpo, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa yayin da ake yi masa magani.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe sojan Najeriya da wani jami'in NSCDC

An adana gawar mamacin a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin, yayin da ’yan sanda suka dauko katin shaidar aikin marigayin a wurin da lamarin ya faru.

Wasu 'yan bindiga sun farmaki amarya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wurin taron bikin aure a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kashe akalla mutane biyu daga tawagar masu zuwa biki a harin yayin da wasu da dama, ciki har da amarya, suka jikkata.

Hakazalika, 'yan bindigan sun yi awon gaba da bakin da suka halarci biki da dama yayin harin wanda suka kai a unguwar Nagunda cikin karamar hukumar Kankara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng