Za a Shafe Kwana 7 ana Makokin Rasuwar Sarkin da Ya Yi Shekara 49 a Karaga

Za a Shafe Kwana 7 ana Makokin Rasuwar Sarkin da Ya Yi Shekara 49 a Karaga

  • Shugaban ƙaramar hukumar Badagry a Legas ya ayyana kwanaki bakwai na jimami bayan rasuwar Akran na masarautar yankin
  • An bayyana cewa marigayi sarkin ya rasu ne bayan dogon mulki mai cike da tarihi da hidima ga al’ummar yankinsa da Legas
  • Hukumomi da jama’a sun fara nuna alhini tare da tunawa da rawar da marigayi Akran ya taka wajen haɗin kai da cigaban al’adu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Shugaban Ƙaramar Hukumar Badagry, Babatunde Hunpe, ya ayyana mako guda na jimami sakamakon rasuwar Akran na Badagry, Aholu Menu Toyi I.

Hunpe ya bayyana hakan ne yayin sanar da mutuwar basaraken a hukumance ta hannun sakataren yaɗa labaransa, inda ya nuna alhini kan rashin da masarautar Badagry ta yi.

Sarkin Badagry Aholu Menu Toyi I
Marigayi Mai martaba Aholu Menu Toyi I. Hoto: Daga Olusegun
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa sanarwar ta zo ne bayan samun amincewar gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, domin bai wa marigayi Akran girmamawar da ta dace da matsayinsa.

Kara karanta wannan

Rasuwar Sarki mai martaba ta taba Bola Tinubu, ya mika ta'aziyya ga masarautar Badagry

Ana jimamin rasuwar Sarkin Badagry a Legas

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce an ayyana kwanaki bakwai na jimami da zaman makoki domin bai wa jama’ar Badagry damar yin nazari da tunawa da rayuwar marigayi sarkin.

Ya buƙaci al’umma su yi dubi kan jagorancinsa na rashin son kai, dabi’un da ya bari, da kuma sadaukarwar da ya yi tsawon rayuwarsa ga ƙaramar hukuma, jihar Legas da Najeriya baki ɗaya.

A cewarsa zaman makokin da aka ayyana wata dama ce ta tuna irin darussan da marigayi Akran ya koyar ta hanyar ayyukansa.

Rayuwa da martabar marigayi Akran

Shugaban karamar hukumar ya bayyana marigayi Akran a matsayin basaraken da ya kawo gagarumin cigaba a tarihin Badagry

The Nation ta rahoto ya ce marigayi sarkin amintaccen mai kare al’ada ne, wanda ya tsaya tsayin daka wajen kiyaye al’adu da mutuncin masarautar Badagry.

Haka kuma, ya bayyana shi a matsayin uba mai tausayi da hikima, wanda shawarwarinsa da karamcinsa suka shafi duk wanda ya kusance shi.

Kara karanta wannan

'Harin sojojin Amurka a Najeriya ya kashe Lakurawa 155,' Rahoto

An yi wa iyalan sarkin ta'aziyya

Shugaban ƙaramar hukumar ya miƙa ta’aziyyarsa ga majalisar sarakuna da hakimai a Badagry da Jihar Legas, da kuma iyalan marigayi Akran da daukacin jama’ar masarautar.

Ya ce mutuwar basaraken babban rashi ne ga Badagry, ganin irin rawar da ya taka wajen zaman lafiya da haɗin kai a yankin.

Hunpe ya jaddada cewa za a ci gaba da girmama tarihin marigayi sarkin ta hanyar kiyaye manufofi da kyawawan dabi’un da ya bari.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya nuna alhini kan rasuwar Akran, yana mai bayyana mutuwar a matsayin rashi mai raɗaɗi ga Badagry, jihar da ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Babajide Sawo-Olu
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu yana jawabi. Hoto: Lagos State Government
Source: Facebook

Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Akran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar Akran na Badagry, Aholu Menu Toyi I.

Shugaban kasar ya bayyana cewa rashin mai martaba Sarkin ya bar babban gibi a yankinsa da kasa baki daya lura da matsayinsa.

Baya ga haka, Bola Tinubu ya tura sakon jaje ga majalisar sarakunan jihar Legas bisa rasa daya daga cikin masu fada a ji a cikinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng