Rasuwar Sarki Mai Martaba Ta Taba Bola Tinubu, Ya Mika Ta'aziyya ga Masarautar Badagry

Rasuwar Sarki Mai Martaba Ta Taba Bola Tinubu, Ya Mika Ta'aziyya ga Masarautar Badagry

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwra Sarkin Badagry da ke jihar Legas, Wheno Aholu Menu-Toyi I, wanda aka fi sani da Oba Babatunde Akran
  • Mai girma shugaban kasa ya tuna da wasu halaye da nagartar marigayi Sarkin, inda ya bukaci mutane su yi koyi da dabi'unsa
  • Shugaba Tinubu ya yi addu'ar Allah ya ji kan mamacin, sannan ya mika ta'aziyya ga iyalan marigayin bisa wannan rashi da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mutuwar Akran na Badagry da ke jihar Legas, Wheno Aholu Menu-Toyi I, ta jefa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu cikin jimami da alhini.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Legas bisa rasuwar Sarkin Badagry, wanda aka fi sani da Oba Babatunde Akran.

Kara karanta wannan

Shirin tsige Gwamna Fubara a Majalisa ya gamu da tangarda, 'yan Majalisa 2 sun canza tunani

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Sarki Babatunde Akran ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin da ta shige, yana da shekaru kusan 90 a duniya.

Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa Legas

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya jajantawa majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Legas.

Marigayin ya kasance mataimakin shugaban majalisar sarakunan jihar Legas, matsayin da ya rike har karshen rayuwarsa.

Haka zalika, shugaban kasa ya mika ta'aziyyarsa ga majalisar hakiman Badagry da kuma daukacin mazauna tsohon birnin na Badagry.

Tinubu ya yabi mulkin Sarkin Badagry

Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa marigayin ya gina jagoranci na gari tare da hangen nesa a cikin mulkinsa na sama da shekaru 40, wanda ya samar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a tsakanin mutanensa.

Shugaban ya jinjina wa kokarin Sarkin wajen kare martabar birnin Badagry, wanda tarihi ya nuna a matsayin tsohuwar tashar cinikin bayi, da kuma daukaka al'adun birnin da suka shahara a idon duniya.

Kara karanta wannan

"Ina ya shiga?" Peter Obi ya fito da damuwarsa game da yawan tafiye tafiyen Tinubu

Har ila yau,Tinubu ya yaba wa hikimar marigayin wajen tafi da al'amuran zamani tare da kiyaye dabi'un gargajiya, da kuma yadda ya tafi da kabilu daban-daban da ke zaune a yankinsa cikin lumana.

Shugaba Tinubu da marigayi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Marigayi Sarkin Badagry, Wheno Aholu Menu-Toyi I Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sakon ta'aziyyar Tinubu ga iyalan Sarkin

Shugaba Tinubu ya yi kira ga jama'a da su yi koyi da kyakkyawan gado da marigayin ya bari, inda ya tuna cewa Oba Babatunde ya yi aikin koyarwa na shekaru da dama kafin ya tsallaka fannin aikin jarida.

"Ya taka rawar gani a gidajen jaridu kamar su West African Pilot, Post Group of Newspapers, Daily Sketch, da kuma New Nigeria," in ji Tinubu.

A karshe, Shugaba Tinubu ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin, sannan ya mika ta'aziyya ga iyalan marigayin biA wannan rashi.

Sarki ya rasu ana shirin karin shekararsa

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Ezineze Mgbidi, Mai Martaba Igwe PD Uzochukwu (Ezudo I na Mgbidi) ya riga mu gidan gaskiya a jihar Enugu.

Bayanai sun nuna cewa Sarkin ya mutu bayan shirye-shiryen bikin karin shekararsa sun yi nisa, har an fara kafa tantuna da allunaa yankin masarautarsa.

Al’ummar yankin sun nuna jimami tare da yin shiru na minti ɗaya domin girmama marigayin yayin wani taron jama’a da aka gudanar a makarantar Mgbidi, jihar Enugu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262