Rigimar Iko: Olubadan Ya 'Kunyata' Sarki Mai Martaba a tsakiyar Taron Jama'a a Najeriya
- An yi wata yar dirama a wurin wani taro da manyan sarakunan kasar Yarbawa biyu suka halarta a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
- Lamarin ya faru ne lokacin da Olubadan na kasar Ibadan ya iso wurin taron, ya zauna a wurin da aka tanadar masa kusa da Alaafin
- Sarakunan gargajiya na Ibadan sun nuna fushinsu kan rashin girmamawar da Alaafin ya nunawa Olubadan a wurin taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, Nigeria - Sarkin Ibadan, Rashidi Ladoja (Olubadan na Ibadanland) da Alaafin na Oyo, Abimbola Owoade, sun sake haifar da ce-ce-ku-ce bayan abin da ya faru a wurin taron addini a Ibadan.
Rahotanni sun nuna cewa manyan sarakunan biyu na neman dawo da tsohuwar gaba da rikicin iko da ya dade yana faruwa tsakaninsu.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa sarakunan biyu masu daraja a kasar Yarbawa sun halarci taron addinai na 2026 da aka gudanar a Grand Space, kusa da majalisar dokokin jihar Oyo.

Kara karanta wannan
"Ina ya shiga?" Peter Obi ya fito da damuwarsa game da yawan tafiye tafiyen Tinubu
Me ya faru tsakanin Olubadan da Alaafin?
Wani bidiyo da ya bazu sosai a kafafen sada zumunta kuma TVC News ta wallafa a Facebook, ya nuna Olubadan yana tafiya zuwa wurin zamansa kusa da Alaafin, wanda ya riga ya iso tun da wuri kuma yana zaune.
Yayin da Ladoja ke karasowa, Owoade ya miƙa masa hannu domin gaisuwa ba tare da ya mike tsaye don girmama shi ba, amma Olubadan ya ƙi amsawa, lamarin da ya sa Alaafin ya janye hannunsa.
Wannan lamari ya sake tayar da tsohuwar rigimar tarihi kan matsayi da fifiko tsakanin manyan kujerun gargajiya biyu na yankin Yarbawa.
Sarakunan Ibadan sun soki dabi'ar Alaafin
Da suke martani kan lamarin, sarakunan gargajiya na Ibadan sun soki abin da Alaafin ya yi, suna bayyana shi a matsayin rashin girmamawa ga Olubadan da kuma masarautar Ibadan.
A cikin wata sanarwa, sarakunan sun ce Ibadanland ba ta ƙarƙashin ikon Alaafin, inda suka ƙara da cewa miƙa wa Olubadan hannu yayin da Alaafin ke zaune cin mutunci ne.
Sun yi kira ga Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da ya gargadi Alaafin kan abin da suka kira “halaye na rashin tarbiyya” da yake nuna wa sarakunan gargajiya na Ibadan.
Sarakuna sun yi barazanar daukar mataki
Sanarwar ta ce:
“Rashin girmamawar Alaafin ga Olubadan da babbar masarautar Ibadan ya wuce kima.
“Idan Gwamna Seyi Makinde bai gargade shi ba, ya bar mutane da suka hada da sarakuna da hakimai su yi maganinsa, to fa duk abin da ya faru kada Alaafin ya zargi kowa ya zargi kansa

Source: Twitter
Sun ce akwai bayanai da dama na abubuwan da suka faru a baya da suke kallon su a matsayin rashin ladabi ga sarakunan gargajiya na Ibadan, tare da gargaɗin cewa Ibadanland ba za ta ci gaba da jurewa ba.
Sun ƙara da cewa bai dace ba Alaafin ya zauna yana miƙa hannu domin gaishe da Olubadan mai shekaru 82 a cikin ƙasar Ibadan ba.
Abin da Olubadan ya fadawa 'yan siyasa
A baya, kun ji cewa Sarkin Ibadan a jihar Oyo, Olubadan na Ibadanlanda, Oba Rashidi Ladoja ya karbi bakuncin manyan yan siyasa a fadarsa.

Kara karanta wannan
Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara
Oba Ladoja, tsohon gwamnan Oyo, ya shaida masu cewa shi ba dan siyasa ba ne yanzu, yana mai jaddada cewa zai yi hidima ga jama’ar Ibadan da Najeriya baki ɗaya.
Ya tuna irin dangantakarsa da Atiku Abubakar a jam’iyyu daban-daban, yana cewa yanzu manufarsa ita ce tabbatar da adalci, da zaman lafiya ga al’ummarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
