Sanata Barau zai Fara Raba Kudi duk Wata a Kano da Kayan Tallafi Daban Daban

Sanata Barau zai Fara Raba Kudi duk Wata a Kano da Kayan Tallafi Daban Daban

  • Sanata Barau Jibrin ya sanar da kammala shirye-shiryen fara wani gagarumin shirin tallafawa jama’a domin bunƙasa tattalin arziki a Kano ta Arewa
  • Shirin zai shafi dubban mutane a fannoni daban-daban kamar sufuri, kasuwanci, mata da matasa, tare da tallafin kuɗi da kayan sana’a a yankinsa
  • An bayyana cewa za a fara aiwatar da shirin ne daga watan Fabrairu zuwa Disamba, 2026, kafin daga bisani a faɗaɗa shi zuwa sauran sassan jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya sanar da ƙaddamar da wani gagarumin shirin tallafawa jama’a da nufin ƙarfafa tattalin arziki da rage raɗaɗin rashin aikin yi.

Sanatan ya bayyana cewa shirin ya biyo bayan ƙoƙarinsa na ci gaba da tallafa wa al’umma, musamman ma matasa da mata, domin su dogara da kansu ta hanyar sana’o’i da ayyukan yi.

Kara karanta wannan

'Harin sojojin Amurka a Najeriya ya kashe Lakurawa 155,' Rahoto

Sanata Barau i. Jibrin
Sanata Barau Jibrin mai wakilatar Kano ta Arewa a majalisa. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, Barau ya ce bayani kan shirin ya fito ne bayan hadimansa, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah da Shitu Madaki Kunchi, suka yi wa manema labarai jawabi a birnin Kano.

Barau Jibrin zai ba da tallafin kudi

An bayyana cewa shirin tallafawa jama’ar zai gudana ne daga watan Fabrairu zuwa Disamba, 2026, inda aka tsara yadda za a rika aiwatar da shi a kowane wata domin tabbatar da adalci da tsari.

A cewar Sanata Barau, shirin zai shafi ƙananan hukumomi 13 da ke cikin Kano ta Arewa, inda kowane wata za a zaɓi mutane 100 daga kowace ƙaramar hukuma don amfana da tallafin kuɗi.

Jimillar mutane 15,600 ne ake sa ran za su karɓi tallafin kuɗi na N100,000 a cikin wata12, domin su fara ko faɗaɗa sana’o’insu.

Tallafin Barau a sufuri da kasuwanci

A ɓangaren sufuri, shirin ya tanadi raba motoci 130 ga ƙungiyoyi daban-daban domin inganta harkokin sufuri a Kano ta Arewa. Haka kuma, za a raba babura 1,000 ga masu sana’ar tuƙi, malamai, ɗalibai da sauran rukunin jama’a.

Kara karanta wannan

Ana maganar shiga APC, Abba Kabir ya caccaki Ganduje, ya yabi Kwankwaso

Sanatan ya ƙara da cewa mata 2,600 za su amfana da rabon injinan ɗinki da injinan nika, domin ƙarfafa sana’o’in hannu da bunƙasa kasuwanci a matakin tushe.

Bugu da ƙari, za a raba injinan sanyaya ruwa da injinan murza taliya tare da raba buhunan fulawa domin taimaka wa ƙananan ‘yan kasuwa a harkokin sarrafa abinci da adana shi.

Tallafin Barau a fannin ilimi da wasanni

A ɓangaren ilimi, an tanadi raba kekuna 1,300 ga yara ‘yan makaranta domin sauƙaƙa musu sufuri da ƙara samun damar zuwa makaranta a kai a kai.

A fannin wasanni kuwa, Sanata Barau ya ce za a raba kayan wasa da rigunan ƙwallon ƙafa ga ƙungiyoyi 1,950, inda za a ware kungiyoyi 150 a kowace ƙaramar hukuma domin bunƙasa wasanni.

Sanata Barau Jibrin a majalisa
Sanata Barau Jibrin yana bayani a majalisa. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Sanatan ya bayyana cewa bayan kammala shirin a Kano ta Arewa, za a faɗaɗa shi zuwa Kano ta Tsakiya da Kano ta Kudu, yana mai cewa manufarsa ita ce kowa ya amfana da shirin.

Gwamna Abba ya raba kayan tallafi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta raba kayan tallafi ga daliban da aka yaye a cibiyoyin koyon sana'a.

Kara karanta wannan

"Bai yi butulci ba": Kwamishina a Kano ya wanke Abba daga zargin juya wa Kwankwaso baya

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an koyar da matasan sana'o'i da suka hada da kiwon kifi, kiwon kaji da sauransu.

Ya kara da cewa an ba kowane matashi kayan aiki da zai fara sana'a domin samun damar dogaro da kai da ciyar da Kano gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng