Yan Ta'adda Sun Shigo da Jirage Marasa Matuka, Za Su Kai Hare Hare Jihohi 2 a Najeriya

Yan Ta'adda Sun Shigo da Jirage Marasa Matuka, Za Su Kai Hare Hare Jihohi 2 a Najeriya

  • An samu wasu bayanan sirri kan makaman da yan ta'adda suka mallaka da kuma shirin da suke yi kan sojojin Najeriya
  • Wasu majiyoyi sun ce kungiyar ISWAP da ta balle daga Boko Haram ta saya sababbin jirage masa matuka fiye da 30 a kasar nan
  • Wannan lamari dai ya nuna bukatar jami'an tsaro musamman sojoji da 'yan sanda su dauki matakin gaggawa don kare rayukan jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - An samu wasu bayanan sirri game da irin jirage marasa matuka da kungiyar yan ta'adda ta SWAP ta mallaka da kuma shirye-shiryen da suke yi.

Wasu bayanai sun nuna cewa ISWAP ta kara fadada bangaren amfani da jirage marasa matuka, kuma an gano shirinta na fara kai wa sojojin Najeriya hare-hare.

Hafsan tsaro.
Babbam hafsan taaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: @DHQNigaeia
Source: Facebook

An gano shirin ISWAP na kai hare-hare

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi wa 'yan bindiga raga raga yayin artabu a Kaduna

Wani rahoton tsaro na sirri da Premium Times ta gani ya nuna cewa ‘yan ta’addan na shirin amfani da Unmanned Aerial Vehicles (UAVs) wajen kai hari kan jami'an tsaro a Yobe da Borno.

Rahoton ya nuna cewa ISWAP na shirin amfani da jiragen UAVs kan rundunonin sojoji da tawagogin jami'an tsaro da ke sintiri a muhimman wuraren a jihohin biyu.

  1. A cewar majiyoyi masu masaniya da lamarin, shugabannin ISWAP sun kammala shirye-shiryen kai hare-haren, in ji rahoton DW.

Wane shiri kungiyar ISWAP ta yi?

Majiyoyin sun bayyana cewa mayaƙan ƙungiyar da ke yankin Timbuktu Triangle da Dajin Sambisa sun karɓi sabon rukunin jirage marasa matuka kimanin 35, waɗanda ake zargin an shigo da su ta Tafkin Chadi.

Jami’an tsaro sun ce kungiyar ta riga ta kammala gwajin tashin jiragen UAV ɗin kuma ta tabbatar da cewa sun shirya aiki.

Wannan lamarin ya ƙara tayar da hankalin sojoji kan yiwuwar ƙaruwa a dabarun yaƙin sari ka noke da kungiyar ta'addancin ta bullo da shi.

A ‘yan shekarun nan, ISWAP ta matsa kaimi wajen amfani fasahar jirage marasa matuka, ko dai don leken asiri ko kai hare-hare.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda 11 sun ji ruwan azaba a hannun sojoji, sun ajiye makamansu a Borno

Dakarun soji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a shingen binciken ababen hawa Goto: @NigeriaArmy
Source: Twitter

Nasarorin da sojoji suka samu a Arewa

A baya-bayan nan dai sojojin Najeriya sun ƙara ƙaimi a ayyukan yaƙi da ta’addanci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, inda suka lalata sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe ko kama manyan shugabanninsu.

Sai dai duk da haka, ƙungiyoyin ‘yan tada ƙayar baya, ciki har da ISWAP da Boko Haram, na ci gaba da sauya dabaru, kamar amfani da bama-baman (IEDs).

Majiyoyin tsaro sun ce wannan bayanan sirri da aka samu tamkar kira ne ga rundunar sojojin Najeriya domin ta daukii mataki tun kafin lokaci ya kure.

Yan ta'adda 11 sun mika wuya a Borno

A wani labarin, kun ji cewa dakaru sojoji sun kashe ’yan ta’adda 8, sun kama masu kai musu kayan abinci da man fetur guda biyu, yayin da wasu miyagun 11.suka miƙa wuya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Kanal Sani Uba , ya fitar a ranar Lahadi, 11 ga Janairu, 2025,

A ranar 10 ga Janairu, 2026, matsin lamba daga dakarun soji a hanyar.Azir zuwa Wajiroko ya tilasta wa mayakan Boko Haram/ISWAP guda 11 mika wuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262