Wata Sabuwa: An Bankado Shirin Raba Wike da Duniya, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

Wata Sabuwa: An Bankado Shirin Raba Wike da Duniya, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • An bankado wata makarkashiyar shirin kashe Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike yayin da ake ci gaba da rikicin siyasa a jihar Rivers
  • Rundunar 'yan sanda ta yi caraf da wani fasto bisa zargin da hannunsa a cikin shirin kulla makarkashiyar kashe tsohon gwamnan na jihar Rivers
  • Hakazalika, bincike ya sanya an tura takardar gayyata ga tsohon sakataren gwamnatin jihar Rivers kuma tsohon Ministan harkokin wasanni a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Rundunar ’yan sandan jihar Rivers ta tsare wani fasto mai zama a Port Harcourt, Tombari Joseph Gbeneol kan zargin hannu a shirin raba Nyesom Wike da duniya.

Rundunar 'yan sandan ta tsare Tombari Joseph Gbeneol ne bisa zargin kulla makarkashiyar kashe Ministan na babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Shugaban jam'iyyar APC da wasu manyan 'yan siyasa 2 sun mutu

'Yan sanda sun bankado shirin kashe Nyesom Wike
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Jaridar Leadership rundunar ta kuma gayyaci tsohon sakataren gwamnatin jihar Rivers (SSG) kuma tsohon Ministan wasanni, Dakta Tammy Danagogo, domin amsa tambayoyi.

Meyasa 'yan sanda suka kama fasto?

Kama faston ya biyo bayan bibiyar wata tattaunawar waya da aka ce ta gudana tsakanin Gbeneol da tsohon SSG, Dakta Tammy Danagogo.

A cikin tattaunawar da aka nadi sautin murya, ana zargin cewa sun tattauna shirin shigo da ’yan kasar Isra’ila domin aiwatar da kashe Ministan na Abuja.

Rahoton jaridar The Nation ya ce tattaunawar ta kare ne da shirin neman tallafin kudi daga gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, domin aiwatar da wannan makarkashiya.

Ana bincike kan shirin kashe Nyesom Wike

Wani babban jami’in tsaro ya ce:

“Abubuwan da ke cikin kiran wayar sun kasance barazana mai tsanani ga tsaron kasa. Wannan ne ya sa sashen IRT ya dauki matakin gaggawa.”

Biyo bayan wannan rahoton sirri, jami’an sashen IRT karkashin jagorancin kwamishinan ’yan sanda, Ahmed Muhammed Sanusi, suka dauki mataki inda suka kama Dakta Gbeneol.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

Rahotanni sun nuna cewa ya shafe kusan makonni biyu yana tsare a hannun jami'an tsaro.

'Yan sanda na binciken yunkurin kashe Nyesom Wike
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

An kitsa shirin kashe Wike

Majiyoyin tsaro sun kuma bayyana cewa ana ci gaba da kokarin kama Dakta Danagogo, wanda ake zargin ya buya tun bayan fitowar lamarin fili.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama wanda ake zargin, inda ta ce yana hannunsu yayin da bincike ke gudana.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta kasa, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamun a ranar Litinin, 12 ga watan Janairun 2026.

“Yana hannunmu. Bincike na gudana.”

- CSP Benjamin Hundeyin

Wike ya amsa wa masu son a kore shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya tanka kan masu bukatar Shugaba Bola Tinubu ya kore shi daga mukaminsa.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakken ’yanci da ikon korarsa daga mukaminsa a duk lokacin da ya ga dama.

Ministan na Abuja ya bayyana cewa goyon bayan da ya ba Shugaba Tinubu a zaben 2023 ya samo asali ne daga yarda da hangen nesan da yake da shi, inda ya kara da cewa ba su taba kulla wata yarjejeniya ta musamman da shugaban kasar ba kafin zaben.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng