'Dole a Sake Shi,' Atiku Ya Harzuka da Aka Garkame Matashin da Ke Sukar Tinubu

'Dole a Sake Shi,' Atiku Ya Harzuka da Aka Garkame Matashin da Ke Sukar Tinubu

  • Yanzu haka dai Abubakar Saleem Musa, hadimin gwamnan Zamfara yana tsare a gidan yarin Keffi saboda sukar gwamnatin Bola Tinubu
  • Atiku Abubakar ya fusata matuka, inda ya ce kama matashin tamkar barazana ce ga dimokuradiyya, don haka 'dole a sake shi'
  • Amnesty International kuwa ta ce ko kadan Salim bai aikata laifi ba, face amfani da hakkin sa na dan kasa wajen bayyana ra'ayin sa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An garkame shahararren mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a kafafen sada zumunta, Abubakar Saleem, wanda aka fi sani da @AM_Saleeeem a kafar X.

Salim dai na tsare ne a gidan gyaran hali na Keffi bayan kama shi da aka yi a ranar 11 ga Janairu, 2026, sakamakon sukar da yake yi wa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi: Shugaban jam'iyyar APC da wasu manyan 'yan siyasa 2 sun mutu

Atiku ya bukaci gwamnatin Tinubu ta saki matashin da aka garkame saboda sukar gwamnati.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu), matashin da aka garkame, Abubakar Saleem (tsakiya) da Atiku Abubakar. Hoto: @officialABAT, @AmnestyNigeria, @atiku
Source: Twitter

An garkame matashi mai sukar Tinubu

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa garkame matashin, wanda hadimi ne ga gwamnan Zamfara, ya janyo gagarumar zanga-zangar nuna bacin rai a yanar gizo.

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ce ta fara fallasa batun kama shi, inda ta bayyana cewa Salim bai aikata wani laifin komai aka garkame shi ba.

A shafinta na X, kungiyar ta yi gargadin cewa ana amfani da karfin iko ne wajen tsoratar da matasa da masu ra'ayin da ya sabawa masu rike da madafun iko domin kulle musu baki.

A cewar Amnesty, matsin lambar da Saleem ke fuskanta wani bangare ne na babban shiri na cin zarafi da tsare matasa ba tare da bin ka’ida ba domin kawai sun fadi ra'ayinsu.

Atiku ya yi Allah-wadai da kama Saleem

Daga cikin manyan mutanen da suka yi magana kan wannan batu har da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Matakai 8 da majalisar Rivers za ta bi domin tsige Gwamna Fubara

A cikin wata sanarwa mai zafi da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki Saleem ba tare da wani sharaɗi ba.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin mayar da Najeriya kasar da babu 'yancin fadin albarkacin baki, inda ake nuna wa masu adawa karfi ta hanyar shari'ar karya.

Atiku ya jaddada cewa babban "laifin" Saleem shi ne kokarin nuna rashin jin dadinsa kan yadda tsaro yake kara lalacewa a Arewacin Najeriya da sauran sassan kasar.

Atiku ya bukaci gwamnatin Tinubu ta saki matashi Abubakar Saleem.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT/Pius Utomi Ekpei
Source: UGC

Atiku ya yi suka kan tauye hakkin jama'a

Atiku ya kara da cewa wannan ba lamari ne da ya shafi mutum guda ba, face dai wani tsari ne da aka fara na kama 'yan jarida, dalibai, har ma da 'yan bautar kasa (NYSC) saboda sukar shugaban kasa ko iyalinsa.

A cewarsa, idan aka bar wannan dabi'a ta ci gaba, harsashin dimokuradiyyar Najeriya zai ruguje baki daya.

A karshe, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga kasashen duniya da su sanya idanu tare da tuhumar gwamnatin Najeriya kan yadda ake tauye hakkin ’yan kasa da kuma saba wa tsarin mulki.

Kara karanta wannan

An 'sace' wani hadimin gwamnan Zamfara, ana zargin akwai sa hannun Nuhu Ribasu

Ya ce kasa ba za ta taba da'awar tana kan tafarkin dimokuradiyya ba matukar ana tsoratar da jami'an yada labarai da sauran masu sharhi kan al'amuran yau da kullum.

An 'sace' hadimin gwamnan jihar Zamfara

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Zamfara ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya sa baki kan abin da ta kira "garkuwa" da Saleem Abubakar, wani hadimin Gwamna Dauda Lawal.

Gamnatin Dauda Lawal ta zargi dakarun tsaro na musamman daga ofishin mai bayar da shawara kan tsaron ƙasa (NSA) da sace Saleem Abubakar ba tare da wani sammacin kotu ba.

Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa Ministan tsaro, Bello Matawalle, ne ya kitsa wannan kamun ta hanyar amfani da ofishin Nuhu Ribadu domin tsoratar da ’yan adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com