'Yan Ta'adda 11 Sun Ji Ruwan Azaba a Hannun Sojoji, Sun Ajiye Makamansu a Borno
- Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kashe yan ta'adda takwas tare da kama wasu miyagu 11 da suka mika wuya a jihar Borno
- Jami'an tsaro sun lalata sansanonin yan ta'adda da dama tare da kwace buhunan taki da ake amfani dasu wajen hada bama-bamai
- Operation Hadin Kai ta sake jaddada kudurin dakarunta na ganin an fatattaki yan ta'adda baki daya tare da dawo da zaman lafiya a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) dake yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas ta sanar da gagarumar nasara a Borno.
OPHK ta ce dakarunta sun kashe ’yan ta’adda 8, sun kama masu kai musu kayan abinci da man fetur guda biyu, yayin da wasu miyagun 11 suka miƙa wuya.

Source: Twitter
Sojoji sun farmaki sansanonin 'yan ta'adda
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar Lahadi, 11 ga Janairu, 2025, a cewar rahoton Punch.
Sani Uba ya bayyana cewa waɗannan nasarori sun biyo bayan matsin lamba da dakarun soji suka yi wa ’yan ta’addan a sassanoninsu daban daban da ke a Jihar Borno.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ya ce kuma bayyana cewa sojoji sun samu nasarar ne ƙarƙashin tsarin aikin soja na Operation Desert Sanity V.
'Yan ta'adda sun mika wuya a Borno
A ranar 10 ga Janairu, 2026, matsin lamba daga dakarun soji a hanyar Azir zuwa Wajiroko ya tilasta wa mayakan Boko Haram/ISWAP guda 11 mika wuya.
Mayakan sun miƙa kansu tare da makamansu ƙirar AK-47 da albarusai masu yawa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
An cafke jami’in DSS da ake zargi ya tursasa wa budurwa barin Musulunci bayan dirka mata ciki
Haka kuma, a ranar 9 ga Janairu, dakarun sun kai samame a yankin Bulaagalda, inda suka lalata sansanonin ’yan ta’adda da dama, har ma da shahararrun sansanonin Abu Nazir da Abu Ahmed.
A yayin wannan samame, sojoji sun ruguza dukkan gine-ginen da ’yan ta’addan ke rayuwa a ciki tare da ƙwace tutocin ƙungiyar da sauran makamai.

Source: Original
Kashe 'yan ta'adda da kama masu tallafa masu
Sauran nasarorin da sojojin suka samu sun haɗa da:
- Kashe mayaka 8: Dakarun sojin sun fafata da mayakan JAS/ISWAP tsakanin ƙauyen Sojiri da Kayamla, inda suka kashe mutane 8 tare da ƙwace bindigogi.
- Kama masu kai masu kaya: An kama mutane biyu a ƙaramar hukumar Gubio waɗanda ake zargi da kai wa ’yan ta’adda kayayyaki da man fetur.
- Kama taki: Sojoji sun tare wata mota a kan iyakar Kamaru da Najeriya ɗauke da buhunan taki (urea) guda 12. Ana amfani da wannan takin ne wajen sarrafa bama-bamai na gida (IEDs).
Rundunar ta tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka kama da kayayyakin da aka samu suna hannun jami'an tsaro don ci gaba da bincike kafin ɗaukar matakin shari'a.

Kara karanta wannan
Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a Borno, an kashe tsageru da dama
An kashe soja da jami'in NSCDC
A wani labari, mun ruwaito cewa, yan bindiga sun kashe soja da jami'in hukumar NSCDC a jihar Benue yayin da suke kan hanyar dawowa daga kasuwa.
Harin ya tilasta wa daruruwan mazauna garin Udeku tserewa daga gidajensu yayin da harkokin yau da kullum suka tsaya cik saboda fargabar wani harin.
Jami'an tsaron da aka kashe na daga cikin dakarun hadin gwiwa da aka tura domin dakile hare-haren makiyaya dake addabar yankunan jihar Benue.
Asali: Legit.ng
