Gwamnati Ta Ware sama da N1bn don Yi wa Gidajen Tinubu, Shettima Kwaskwarima
- Gwamnatin tarayya ta ware N1.07bn a kasafin 2026 domin gyaran gidajen Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima
- Jimilar kuɗin da aka ware don gyaran gidajen Shugaba Tinubu da Mataimakinsa a cikin shekaru uku sun kai Naira biliyan 18.4
- A cikin kudin da aka ci burin batarwa, ana sa ran za a kashe N459.4m domin gyara gidan Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ware kudi, N1.07bn a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin gyaran gine-ginen zama na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
Rahotonni sun nuna cewa wannan kuɗi da aka ware sun ƙara yawan kuɗin da aka tanada don gyaran gidajen shugabannin biyu a cikin shekaru uku zuwa N18.4bn.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wannan na zuwa bayan Tinubu ya gabatar da kasafin 2026, ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya a ranar 19 ga Disamba, 2025.
Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi
Trust radio ta wallafa cewa a baya, Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattawa da ta Wakilai wasika, inda ya nemi soke tare da sake zartar da dokokin kasafin 2024 da 2025.
Jimillar kudin da ke kunshe a cikin kasafin ya kai N43.56trn da N48.32trn, domin tabbatar da an aiwatar da su zuwa 31 ga Maris, 2026.
Kasafin da ke gaban majalisa yanzu ya kai N58.18trn, daga ciki har da N15.52trn na biyan basussukan da aka bin kasar nan.
Ana sa ran samun kudin shiga N34.33trn, lamarin da zai haifar da gibi na N23.85trn, wanda za a cike ta hanyar karɓar rance na cikin gida da na ƙasashen waje.
Kudin da za a kashewa Fadar Shugaban Ƙasa

Kara karanta wannan
Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara
Takardar kasafi da Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya ya wallafa a shafinsa a makon da ya gabata ta nuna cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta ware N459.4m domin “gyara gidan Shugaba Tinubu.

Source: Twitter
Haka kuma ya fitar da bayanin cewa an ware Naira miliyan 615.5 ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Shettima.
A shekarar da ta gabata, an ware N1.53bn, inda N879.3m suka tafi ga gyaran gidan Shugaban Ƙasa, sai N656.4m ga na Mataimakin Shugaban Ƙasa.
A 2024 kuma, an tanadi N1.3bn don wannan gyare-gyare. Haka kuma, an ware N300m a 2024, N466m a 2025, da N326.8m a 2026 don gyaran masaukin Mataimakin Shugaban Ƙasa a Fadar Aso Rock.
An ware kudin tafiye-tafiyen Shugaban Ƙasa
A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ware makudan kuɗi a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin tafiye-tafiyen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cikin gida da na kasashen waje.
Takardun kasafin da aka gabatar sun nuna cewa za a kashe Naira biliyan 6.14 ne kai tsaye kan tafiye-tafiyen kasashen waje na Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Haka kuma, an kara Naira miliyan 873.88 domin tafiye-tafiyen cikin gida, lamarin da ya kai jimillar kuɗin tafiye-tafiyen Shugaban Kasa, Tinubu zuwa Naira biliyan 7.01.
Asali: Legit.ng
