Lai Mohammed Ya Fadi Yadda Tsohon Minista Ya Munafurce Shi a gaban Buhari
- Tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, ya bayyana yadda wani minista a zamanin Muhammadu Buhari ya munafurce shi
- Lai Mohammed ya ce mutumin ya ci dunduniyarsa ne a taron majalisar zartarwa, FEC da ake yi kowane mako a birnin Abuja
- Ya bayyana cewa marigayi Buhari ya kare shi kai tsaye, yana yabon rawar da yake takawa wajen kare gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana yadda wani abokin aikinsa ya ci dunduniyarsa.
Lai Mohammed ya ce tsohon ministan ya yi gulmarsa a majalisar ministocin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
Yadda ministan Buhari ya soki Lai Mohammed
Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa mai taken “Headlines and Soundbites: Media Moments that Defined an Administration”, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Wike ya maida martani ga masu bukatar Tinubu ya tsige shi daga kujerar Ministan Abuja
A cewarsa, tsohon ministan wanda bai ambaci sunansa ba amma ya ce daga yankin Kudu maso Yamma yake, ya zarge shi da rashin iya aiki, duk da sanin cewa ba ya nan a taron.
Mohammed ya ce a lokacin yana Washington DC ne, inda yake gudanar da muhimman ganawa da kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da cibiyoyin nazari.
Ya ce, daga baya ya samu labarin cewa ministan ya yi ƙorafi yana cewa duk da cewa gwamnati na aiki tukuru, Ministan Yaɗa Labarai ba ya yin isasshen ƙoƙari wajen tallata nasarorin gwamnati.
Sai dai, Lai Mohammed ya ce Buhari bai amince da wannan magana ba ko kaɗan, ya ce marigayin ya katse taron nan take, inda ya kare shi a gaban majalisar.

Source: Facebook
Yadda Buhari ya yabawa Lai Mohammed
A cewarsa, Buhari ya shaida wa ’yan majalisar cewa yana kallon yadda Lai Mohammed ke kare manufofin gwamnati da bayyana nasarorinta a kafafen yaɗa labarai na duniya.
Ya ce Buhari ya bayyana cewa yana gamsuwa da aikinsa, yana mai cewa babu wata kariya da ta fi wannan, Punch ta ruwaito.
Mohammed ya kara da cewa a tsawon lokacin da yake minista, Buhari ba wai kawai yana yaba masa idan ya yi abin kirki ba ne, har ma yana tsayawa ya kare shi idan aka zarge shi.
A cikin littafin, ya kuma ba da labarin yadda aka kai masa ƙorafi a gaban Buhari, amma Shugaban Ƙasar ya ce:
“Lai? Ban yarda da wannan ba.”
Duk da haka, Buhari ya amince a binciki lamarin, inda daga bisani aka tabbatar da cewa Mohammed ba shi da laifi.
Lai Mohammed ya magantu kan dakatar da X
A baya, kun ji cewa tsohon ministan yada labarai, Lai Mohammed, ya ce dakatar da amfani da Twitter (X) a 2021 na ɗaya daga cikin matakai mafi nauyi da ya taɓa yanke wa.
Ya bayyana cewa tsaron ƙasa ne ya rinjayi duk wata illa da matakin zai iya haifarwa ga ’yan kasuwa da masu amfani da kafar a Najeriya.
Lai Mohammed ya ce shawarar ba ta da alaƙa da goge sakon tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, sabanin rade-radin da suka bazu a lokacin.
Asali: Legit.ng
