Lamari Ya Kazanta: Kansila da Mutane 10 Sun Mutu yayin Kazamin Rikici a Taraba

Lamari Ya Kazanta: Kansila da Mutane 10 Sun Mutu yayin Kazamin Rikici a Taraba

  • Akalla mutane 10 suka rasa rayukansu bayan barkewar rikicin kabilanci a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas
  • Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da kansila mai ci a rikici tsakanin manoma da makiyaya a Gundom, karamar hukumar Donga
  • Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne bayan wani makiyayi ya shigar da shanunsa gona, inda aka kama shi daga bisani aka kashe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Donga, Taraba - Akalla mutane sama da 10 suka mutu yayin wani rikici tsakanin manona da makiyaya a jihar Taraba.

Cikin wadanda suka mutu har da wani kansila mai ci lamarin da tayar da hankula game tsaro a yankin.

Kansila da mutane 10 sun mutu a Taraba
Taswirar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas. Hoto: Legit.
Source: Original

Rikicin makiyaya, manoma ya lakume rayuka

Rahoton Daily Trust ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Donga ta jihar Taraba a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Hajjin 2026: Kano ta tura tawaga Saudiyya domin duba masaukin alhazai

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai kansilan da ke wakiltar mazabar Akete a majalisar karamar hukumar Donga, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Rikicin manoma da makiyaya na daga cikin matsalolin da ke jawo rasa rayukan al'umma da asarar duniyoyi a Najeriya baki daya.

A kullum, hukumomi na ci gaba da daukar alkawarin cewa za su kawo karshen matsalar amma kamar kara rura wutar rikicin ake yi a kullum.

Abin da mazauna yankin ke fada

Wani mazaunin garin Donga mai suna Lawal Adamu ya shaida cewa rikicin ya barke ne a ranar Asabar 10 ga watan Janairun 2026 a kauyen Gundom.

Lawal ya ce matsalar ta fara ne bayan wani makiyayi ya shigar da shanunsa cikin gona, lamarin da ya jawo lalata amfanin gona na manoma.

A cewarsa, fusatattun mazauna kauyen sun kama makiyayin tare da kashe shi, abin da ya haddasa ramuwar gayya tsakanin manoma da makiyaya.

Ya kara da cewa rikicin ya rikide zuwa tashin hankali mai tsanani, inda aka kashe mutane sama da 10 ciki har da kansilan yankin.

Kara karanta wannan

Wike ya maida martani ga masu bukatar Tinubu ya tsige shi daga kujerar Ministan Abuja

Lawal ya bayyana cewa har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu daga bangarorin biyu ba a lokacin hada wannan rahoto.

Rikicin makiyaya da manoma ya yi ajalin mutane 10 a Taraba
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Abin da yan sanda suka ce kan rikicin

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Victor Mshelizah, ya tabbatar da faruwar rikicin a yankin Donga.

Sai dai ya ce ’yan sanda sun gano gawar mutane uku ne kawai da kuma wata mata daya da ta samu raunuka a wurin dalilin rikicin da ya barke.

Mshelizah ya ce jami’an tsaro karkashin jagorancin DPO na Donga suna ci gaba da bincike a dazuka domin gano ko akwai karin gawarwaki.

Wani dan yankin ya bayyanawa wakilin Legit Hausa yadda lamarin ya faru tare da addu'ar samun zaman lafiya.

Dangana Victor ya ce a kusa da su daman ana yawan samun rigima tsakanin Tiv da kuma Fulani wanda ke jawo asarar rayuwa.

Ya ce:

"Daman ana rigima tsakanin Fulani da Tiv wanda ke jawo asarar rayuwa da dukiyoyi, hakan ya faru bayan kashe wani makiyayi wanda su kuma suka dauki fansa."

Kara karanta wannan

Farashin abinci: Manoma sun soki gwamnati da rashin adalci, sun shiga ɗimuwa

Makiyaya sun mamaye garuruwan Benue

Kun ji cewa bakin makiyaya dauke da makamai sun mamaye wasu yankunan jihar Benue, lamarin da ya jefa mutane a cikin tashin hankali.

Shugabannin al'umma sun yi kira ga gwamnati da ta tura jami'an tsaro cikin gaggawa a wadannan yankunan don kare rayukan jama'a da dama.

Mazauna wadannan yankuna sun bayyana yadda suka tsorota biyo bayan wassu hare-hare da ake zargin yan ta'addan ne suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.