An Sake Kai Hari kan Hausawa kusa da Uromi, an Fatattake Su bayan Yanka Awaki
- Fusatattun matasa sun kori ’yan kasuwar Hausawa a kasuwar dabbobi ta Ekpoma, inda suka yanka awaki sakamakon zanga-zanga
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kira da a kwantar da hankali domin kauce wa ramuwar gayya
- ’Yan sanda sun ce an ceto mutane tara da aka sace bayan amfani da na’ura inda aka tilasta masu garkuwa tserewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Wasu fusatattun matasa sun kai hari kasuwar sayar da dabbobi da ke Ekpoma a yankin Edo ta Tsakiya, inda suka kori ’yan kasuwar Hausawa tare da yanka awakin da suka mallaka a ranar Asabar.
Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da mazauna yankin suka gudanar bayan an gano gawar wani matashi da ake zargin masu garkuwa da mutane sun kashe shi a yankin.

Source: Twitter
Matasasun tarwatsa Hausawa a Edo
A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga matasan suna kai hari a kasuwar dabbobi, suna yanka awaki tare da korar ’yan kasuwar daga wurin, cewar Punch.
An ga ’yan kasuwar suna tserewa domin tsira da rayukansu, yayin da shanunsu ke yawo a kan babbar hanya ba tare da jagora ba, inda wasu mazauna yankin ke dukansu.
Wasu daga cikin awakin da aka yanka, fusatattun mazauna yankin sun ja su suka tafi da su.
A cikin wani bidiyo, an ji muryar wani mutum yana cewa:
“Yan Arewa za su dandana", sun kashe awakin nasu kuma har yanzu ana cigaba da kashe su. Ku ga yadda ake dukar shanunsu.”
Kwamishinan Yada Labarai da Tsare-tsare na Jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi Allah-wadai da wannan lamari, tare da kira ga jama’a da su kwantar da hankali domin kauce wa ramuwar gayya a wasu yankuna.
Ya bayyana cewa Gwamna Monday Okpebholo ya riga ya isa Ekpoma domin rokon jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mai bayyana harin a matsayin aikin tarzoma marar dalili.
Ya ce:
“Wannan abu ne da ba ya dacewa ba kwata-kwata. Abin takaici, wasu daga cikin shanun mallakin ’yan jihar ne. Muna kira da a kwantar da hankali domin kauce wa ramuwar gayya. Wannan aiki ne na tarzoma, wanda yawanci ba shi da tunani.”
Rahotanni sun ce mazauna Ekpoma sun rufe hanyoyin shiga da fita garin a ranar Asabar, inda suka nemi jami’an tsaro da su dauki matakan magance matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa kisan matashin da aka gano gawarsa a daji ne ya haddasa zanga-zangar.
Ya ce satar mutane ta zama babbar matsala a yankin, inda manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, yayin da jama’a ke rayuwa cikin fargaba.

Source: Original
Kokarin yan sanda kan zanga-zanga a Edo
Zanga-zangar ta kuma hana gudanar da harkokin kasuwanci, tare da rushe allunan kamfen na zaben 2027 da aka kafa a yankin.
Babban jami’in tsaron gwamnan jihar, Austin Eigbiremolen, ya tabbatar wa jama’a cewa za a tura isassun jami’an tsaro zuwa Ekpoma domin korar masu garkuwa da mutane.
Hakazalika, kakakin rundunar ’yan sandan Edo, Eno Ikoedem, ta ce rundunar ba ta yi ko-in-kula da matsalar tsaron Ekpoma ba.
An yi wa Hausawa kisan gilla a Edo
A baya, kun ji cewa an kashe wasu matafiya 16 daga Arewacin Najeriya sakamakon zargi maras tushe da aka yi musu a jihar Edo.
‘Yan sa-kai sun zarge su da laifin garkuwa da mutane, lamarin da ya haddasa kashe su ba tare da bincike ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.
Asali: Legit.ng


