Borno: Boko Haram Ta Saki Bidiyon Tsohon Mataimakin Ciyaman da Ta Sace

Borno: Boko Haram Ta Saki Bidiyon Tsohon Mataimakin Ciyaman da Ta Sace

  • Yan ta'addan sun fitar da wani sabon bidiyo da ke nuna wasu mutane biyu da ake zargin Boko Haram/ISWAP sun sace mutum biyu a Borno
  • Daya daga mutanen da aka yi garkuwa da su akwai Hon. Hassan Biu Miringa, tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Biu a Borno
  • ‘Yan ta’addan sun bukaci kudin fansa Dala 150,000 ga kowane mutumin da ke hannunsu , wanda ya tashi jimilla $300,000, kimanin N423m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Wani sabon bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta, inda ake ganin wasu maza biyu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP sun sace a Jihar Borno suna roƙon a ceto su.

A bidiyon, mutanen sun bayyana halin da suke ciki tare da neman taimako daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin a taimaka a kubutar da su.

Kara karanta wannan

Halin da masu zuwa Mauludi suke ciki bayan kwashe kwanaki hannun 'yan bindiga a Plateau

Boko Haram ta sace tsohon Mataimakin Ciyaman na Biu
Taswirar jihar Borno, inda aka sace tsohon Mataimakin Ciyaman Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa ɗaya daga cikin wadanda aka sace, Hon. Hassan Biu Miringa, tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Biu ne.

Boko Haram ta sace mutum 2 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da mutane biyun a ranar 17 ga Disamba, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Miringa zuwa Maiduguri a Borno.

A cewarsu, an tare su ne a kusan 2.30 na rana, kuma duk da mawuyacin halin da suke ciki, sun tabbatar da cewa suna raye, suna kuma fatan za a ceto su a cikin gaggawa.

Sun ce:

“An yi garkuwa da mu ne a hanyarmu daga Miringa zuwa Maiduguri kusan karfe 2:30. Alhamdulillah muna raye."

Ya kara da cewa suna kira ga gwamnati da dukkanin masu hali da su taimaka wajen kubutar da su daga hannun miyagun mutanen.

Fansar da Boko Haram ta nema

A cikin bidiyon, wadanda aka sace sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun bukaci kudin fansa Dala 150,000 ga kowane mutum. Hakan na nufin jimillar dala $300,000, wanda ya kai kimanin N423m, domin a sake su.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari 'wurin shakatawa' na gwamnatin tarayya

Sun kuma yi kira kai tsaye ga wasu manyan jami’ai da ‘yan siyasa daga yankin, ciki har da mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur su kawo masu ɗauki.

Mutanen da aka sace sun nemi ɗaukin jami'an gwamnati
Gwamnan jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum Hoto: The Governor of Borno state
Source: Twitter

Haka kuma sun roki Hon. Mukhtar Betara Aliyu, Hon. Sule Ali Rimi, Hon. Yakubu Gambo Kimba, da Alhaji Musa Dogo Biu, da su shiga tsakani domin a ceto su.

Sun ce:

“Muna roƙonsu da su taimaka mana, su zo su ceto mu. Mu ‘ya’yansu ne."

Ya kara da cewa burinsu shi ne a sake su domin su koma su hadu da iyalansu a cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya.

Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro ko gwamnatin jihar kan matakin da ake dauka dangane da wannan sabon bidiyon da bukatar kudin fansa.

Sojoji sun kama hannu a harin Borno

A baya, mun wallafa a cewa sojojin rundunar 'Operation Hadin Kai' (OPHK) sun gano tare da cafke Shariff Umar, da zargin alaka da kai hari Maiduguri a jihar Borno.

Sharif wanda aka fi sani da Yusuf, na daga cikin n manyan masu tsarawa da jagorantar hare-haren kunar bakin wake a Borno, lamarin da ke jefa jama'a a cikin fargaba.

Ana zargin jagoran dai na da hannu kan kai hare-hare da yunkurin kai hare-hare da aka kai kwanan nan a yankin Arewa maso Gabas, daga ciki har da wani masallaci a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng