Jirgin Sama daga Kasar Saudiyya Ya Gamu da Babbar Matsala yayin Sauka a Jihar Kano
- Wasu musulmi da suka dawo daga aikin Umrah a Saudiyya sun gamu da cikas yayin sauka a filin jirgin Kano, an karkatar da su zuwa Abuja
- Rahoto ya nuna cewa bayan jirgin saman ya sauka a Abuja, ya bar mutanen da ya dauko a ciki har na tsawon awanni biyar
- Fasinjojin sun yi kira ga hukumomin NCAA da FAAN su taimaka su shiga tsakani domin suna bukatar fitowa daga jirgin saman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wasu musulmai da suka dawo daga Umrah a Saudiyya su gamu da tangarda yayin da jirgin da ya dauko su zai sauka a jihar Kano.
Rahoto ya nuna cewa rashin kyaun yanayi ya sa aka karkata da akalar jirgin sama zuwa Abuja maimakon sauka a Kano kamar yadda aka tsara masa.

Source: Getty Images
Leadership ta ce fasinjojin da ke dawowa daga kasar Saudiyya sun makale na tsawon kusan awa biyar a cikin jirgin Saudi Arabian Airlines a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja,
Dalilin karkatar da jirgin sama zuwa Abuja
An tsara jirgin zai sauka a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano, amma aka karkatar da shi zuwa Abuja a matsayin matakin kariya bayan samun rahoton yanayin iska da hadari a Kano.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya sauka a Abuja da misalin karfe 1:00 na rana a yau Asabar, amma fasinjojin suka ci gaba da zama a cikin jirgin na fiye da awa biyar ba tare da an bude su.
Abin da fasinjojin suka ce a Abuja
Wasu daga cikin fasinjojin sun shaida wa PRNigeria ta wayar tarho cewa an barsu a cikin jirgin ba tare da abinci, ruwa, ko cikakken bayani daga kamfanin jirgin ba, inda suka bayyana lamarin a matsayin rashin tausayi da cin zarafi.
“Mun fahimci dalilin karkatar da jirgin domin tsaro, amma rufe mu a jirgin na fiye da awa biyar ba tare da wani bayani ko kulawa ta asali ba, kuskure ne da ba za su dauka ba,” in ji wani fasinja.

Source: Getty Images
Fasinjojin sun kuma nuna damuwa kan lafiyar mutanen da ke cikin jirgin, musamman tsofaffin da sauran wadanda suka riga suka gaji sakamakon doguwar tafiya.
“Wasu daga cikin ’yan uwanmu suna rashin lafiya a halin yanzu a cikin jirgin. Gajiyar tafiya da wannan jinkiri mai tsawo tare da rashin taimako na kara jefa mutane cikin wahala. Abin takaici ne kuma wulakanci.”
Sun yi kira ga Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da kuma Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da su gaggauta shiga tsakani, ta hanyar sauke su daga jirgin.
Jirgin sama ya yi hatsari a Owerri
A wani labarin, kun ji cewa wani karamin jirgin sama kirar Cessna 172 ya gamu da hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya samu tangarda tun a sararin samaniya.
An ce jirgin ya yi hatsari ne a filin jirgin kasa da kasa na Sam Mbakwe da ke Owerri, jihar Imo, yayin da yake kokarin sauka.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi ne daga filin jirgin sama na Kaduna zuwa Port Harcourt , kafin matukan jirgin su sanar da cewa sun samu matsala
Asali: Legit.ng

