Gidauniya daga Saudiyya Ta Gina Abubuwan da Za Su Amfani Musulmi a Jihar Kano

Gidauniya daga Saudiyya Ta Gina Abubuwan da Za Su Amfani Musulmi a Jihar Kano

  • Gidauniyar Albidairi daga kasar Saudiyya ta gina gidan marayu da babban masallaci a jihar Kano domin taimaka wa Musulmai
  • A cewar gidauniyar, ta gina gidan marayun ne don tallafa wa yara marasa galihu da kuma magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta
  • Gwamnatin Kano ta yabawa wannan gidauniya, tana mai cewa ta yi abin da ya dace duba da yawan yaran da ba su zuwa makaranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wata gidauniya daga kasar Saudiyya, wacce ke ayyukan jin kai da taimako ta kaddamar da gidan kula da marayu mai daukar yara 700 da masallaci mai daukar mutane 5,000 a Jihar Kano.

Gidauniyar mai suna 'Albidairi Foundation' ta yi wannan aikin alheri na gina masallaci da gidan marayu ne ne a yankin Langel da ke Karamar Hukumar Tofa, a Kano.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ce an rada wa gidan marayun suna Albidairi Orphanage Home kuma a cewar gidauniyar, ta gina shi ne don tallafa wa yara marasa galihu da kuma magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

An bude sabon gidan marayu a Kano

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban gidan marayun, Sheikh Adam Yushau Adam, ya ce Abu-Abdurrahman Al-Bidairi ne ya kafa gidan marayun karkashin gidauniyar Albidairi, wadda aka yi wa rajista a Najeriya.

Ya bayyana cewa an tsara gidan domin daukar yara 14 a kowanne daki, inda kowanne daki ke da bandaki, mai kula da yara, da malamai da za su koyar da ilimin addinin Musulunci da kuma ilimin boko.

“Yaran za su haddace Alkur’ani a nan, sannan an tanadi wuraren motsa jiki. Wurin yana amfani da wutar lantarki ta hasken rana, tare da isasshen tsaro,” in ji shi.

Gwamnatin Kano ta yaba da wannan aiki

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Ilimi, Ali Haruna Makoda, ya wakilta, ya bayyana wannan tallafi a matsayin wanda ya zo a kan lokaci.

Ya ce Jihar Kano na da mafi yawan yara da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, sannan tabarbarewar tsaro a jihohin makwabta ya haifar da yawaitar zawarawa da marayu.

“Irin wadannan cibiyoyi za su taimaka wajen rage wadannan matsaloli da kuma dakile miyagun dabi’u a cikin al’umma,” in ji shi.
Sabon masallaci.
Yadda jama'a suka halarci bide gidan marayu da masallacin da gidauniyar Albidairi ta gina a Kano Hoto: Albidairi Foundation
Source: Facebook

Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman, Hajiya Amina Abdullahi Sani, ta ce gidan marayun zai rage wa gwamnati nauyi.

Amina HOD ta jaddada cewa gwamnati ta kara kaimi wajen tantancewa da amincewa da gidajen marayu na doka, tare da dakile masu aiki ba bisa ka’ida ba, rahoton Daily Post.

Sanatan Bauchi ya gina masallaci

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Buba Umar ya gina katafaren masallaci, makarantar islamiyya da wurin ibada na musamman domin mata a jihar Bauchi.

Sanata Shehu Buba ya yi wannan babban aiki ne a unguwar Nabordo, hedkwatar Masarautar Jema’a da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Sanatan ya bayyana cewa akwai ayyukan jin ƙai da yake aiwatarwa a fadin mazabarsa da ma wajen ta, domin tallafa wa rayuwar talakawan ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262