An Cafke Jami’in DSS da Ake Zargi Ya Tursasa wa Budurwa Barin Musulunci bayan Dirka Mata Ciki

An Cafke Jami’in DSS da Ake Zargi Ya Tursasa wa Budurwa Barin Musulunci bayan Dirka Mata Ciki

  • Hukumar DSS ta yi martani game da zargin wani daga cikin jami'anta da ake yi cewa ya sace wata budurwa tare da sauya mata addini
  • DSS ta tabbatar da cafke wannan jami’inta da aka ce ya dauke yarinya ‘yar shekara 16 tare da tilasta mata sauya addini zuwa Kiristanci
  • Kotun majistare a Hadejia ta bayar da umarnin kama jami’in bayan korafin lauyoyi da ke wakiltar mahaifin yarinyar, Walida Ibrahim

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta yi karin haske kan batun sacewa da lalata wata yarinya mai karancin shekaru da ake zargin wani jami’inta ya aikata.

Kotun majistare da ke Hadejia a Jigawa ta bayar da umarnin kama tare da binciken jami’in DSS kan zargin sacewa, tsare yarinya ba bisa ka’ida ba, da kuma tilasta mata sauya addini tana da shekaru 16.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Kotu ta ba da umarnin wucin gadi a shari'ar gwamnati da likitoci

DSS ta cafke jami'inta da ake zargin ya tilasta wa budurwa barin Musulunci
Shugaban hukumar DSS, Adeola Ajayi. Hoto: DSS Unofficial.
Source: Facebook

Ana zargin jami'in DSS da sace budurwa a Jigawa

Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin yanar gizo a ranar Juma'a 9 ga watan Janairun 2026.

Wannan umarni ya biyo bayan ƙorafin da wata ƙungiyar lauyoyi karkashin Gamji Lawchain suka shigar, inda suka wakilci mahaifin yarinyar mai suna Walida Ibrahim.

A cikin ƙorafin, lauyoyin sun ce jami’in ya sace Walida sama da shekaru biyu da suka wuce, ya tsare ta ba bisa ka’ida ba, ya yi lalata da ita, sannan ya tilasta mata sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci ba tare da izinin iyayenta ba.

Haka kuma sun ce ta haifi ɗa duk da karancin shekaru da take da shi wanda ya kara jawo maganganu, cewar Punch.

Masu shigar da ƙorafin sun yi Allah wadai da abin da suka kira cin zarafin, inda suka bukaci a dakatar, a kama tare da gurfanar da jami’in bayan lalata mata rayuwa.

Kara karanta wannan

Kotu ta nemi cafke jami’in SSS kan sace 'yar yarinya, ya canza mata addini ya aure

Lauyoyin sun kuma bayyana cewa abin da ya faru ya jefa iyalin Walida cikin matsanancin damuwa, lamarin da suka ce ya jawo mutuwar mahaifiyarta.

Ana zargin jami'in DSS da dirka wa budurwa ciki
Taswirar jihar Jigawa da ake zargin jami'in DSS da tilasta wa budurwa barin Musulunci. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da Hukumar DSS ta ce

Da take martani cikin wata sanarwa, Mataimakiyar Daraktan Hulda da Jama’a da Sadarwa ta DSS a hedikwatar ƙasa, Favour Dozie, ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Ta kuma bayyana cewa sunan jami’in da ke cikin lamarin shi ne Ifeanyi Onyewuenyi, ba Ifeanyi Festus kamar yadda aka rubuta a cikin ƙorafin ba.

Sanarwar ta ce:

"Hukumar DSS ta samu rahotannin da ke zargin wani jami’inmu, Ifeanyi Festus, da sacewa, lalata da yarinya ƙarama da cin zarafinta.
“Don fayyacewa, hukumar DSS ba ta da wani jami’i mai suna Ifeanyi Festus a cikin ma’aikatanta.
“Amma mun tabbatar da cewa akwai wani jami’i mai aiki, Ifeanyi Onyewuenyi, wanda ake zargi da tilasta sauya addini tare da aurar da Walida Abdulhadi.”

Sanarwar ta jaddada cewa irin wadannan ayyuka sun saba wa dokoki da ƙa’idojin hukumar DSS, tare da tabbatar da cewa za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

Malami ya musanta cewa DSS sun cafke shi

Mun ba ku labarin cewa wasu rahotanni sun yada cewa Hukumar DSS ta cafke malamin addinin Musulunci a jihar Osun bayan yada bidiyonsa kan Falasɗinu.

An ce an kama Sheikh Daood Imran Molaasan, shugaban wata kungiyar Musulunci a Iwo, Osun, bayan wani bidiyon goyon bayan Falasɗinu.

Sai dai shafin malamin ya fito ya yi karyata rahoton da ake yadawa domin kwantar wa al'umma hankali game da lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.