Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Tsageru da Dama

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Tsageru da Dama

  • 'Yan ta'adda sun ji babu dadi bayan dakarun sojojin sama sun yi musu ruwan wuta a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Dakarun sojojin saman sun jefa bama-bamai kan maboyar 'yan ta'addan da ke yankin Abbaga Jiri a Timbuktu Triangle
  • Bama-baman da sojojin suka jefa kan 'yan ta'addan sun yi nasarar kashe tsageru da dama tare da lalata wuraren boye kayan aikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Sojojin Sama na Najeriya da ke aiki a karkashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, sun kai hare-hare kan 'yan ta'adda a Borno.

Sojojin sun samu nasara bayan kai harin sama na musamman kan 'yan ta'adda a yankin Abbaga Jiri, cikin yankin Timbuktu Triangle na jihar Borno.

Sojojin sama sun tarwatsa 'yan ta'adda a Borno
Jiragen sojojin saman Najeriya a sararin samaniya Hoto: Sodiq Adelakun
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ce daraktan hulɗa da yaɗa labarai na hedikwatar sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Nentawe: Shugaban APC ya kausasa harshe kan hare haren 'yan ta'adda a Neja

Sojojin sama sun samu nasara kan 'yan ta'adda

Ya ce nasarar ta samu ne bayan bayanan sirri daga tushe da dama da suka tabbatar da kasancewar ’yan ta’adda, gine-ginensu, da kuma wuraren ɓoye kayan aiki a yankin.

A cewar sanarwar, bayan tabbatar da sahihin bayanan sirri, jiragen sojojin sama sun shiga aiki ta hanyar leken asiri da kuma kai hare-haren da suka dace kan wuraren da aka gano.

“An kai farmaki ne domin raunana karfin ’yan ta’adda, hana su samun mafaka, da kuma share wa sojojin kasa hanya, tare da bin ka’idojin aikin soja da kuma kare rayukan fararen hula.”

- Ehimen Ejodame

Babban hafsan sojojin sama ya yi tsokaci

Da yake tsokaci kan nasarar aikin, Babban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Sunday Aneke, ya ce nasarar ta nuna kudirinsu na mamaye sararin samaniya domin tallafa wa ayyukan haɗin gwiwa na sojoji, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da hakan.

“Wannan aiki ya nuna jajircewarmu ta amfani da kayan aiki cikin tsari da daidaito domin tallafa wa sojojin kasa. Za mu ci gaba da hana ’yan ta’adda samun ’yancin motsawa, wuraren ɓoyewa da hanyoyin samun kayan aiki a duk inda suka buya.”

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake ta'addanci a Neja awanni bayan kashe mutane

“An kai farmaki cikin nasara kan gine-ginen ’yan ta’adda da aka gano tare da lalata su gaba ɗaya, lamarin da ya hana su ’yancin aikata ayyukansu."
"Haka kuma, wani karin farmaki ya hallaka ’yan ta’adda masu makamai da aka hango suna taruwa a wurin.”

- Air Marshal Kelvin Aneke

Sojojin sama sun samu nasara kan 'yan ta'adda

A cewarsa, shigar sojojin kasa daga baya cikin yankin ya tabbatar da ingancin hare-haren sama da kuma nasarar aikin haɗin gwiwar sojojin sama da na kasa.

Sojojin sama sun jefa bama-bamai kan 'yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Air Marshal Aneke ya kuma jaddada cewa:

“Ayyukanmu na sama za su ci gaba da kasancewa masu tsauri kuma bisa ingantattun bayanan sirri. Ana tsara su ne cikin tsari domin cimma sakamako mai girma kan ’yan ta’adda tare da kare fararen hula."
"Rundunar sojojin sama ta Najeriya za ta ci gaba da matsa lamba har sai an rusa dukkan hanyoyin 'yan ta'adda ke amfani da su gaba ɗaya.”

Dakarun Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun yi raga-raga da 'yan bindiga a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga: Sojoji sun yi ruwan bama bamai a Kano, an kashe miyagu 23

Dakarun sojojin saman na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga 23 bayan sun jefa musu bama-bamai.

'Yan bindigan dai sun tsere ne daga jihar Kano bayan sun kai hare-hare a kananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng