Sanata Shehu Buba Ya Gina Katafaren Masallaci na Maza da Mata don Yada Musulunci

Sanata Shehu Buba Ya Gina Katafaren Masallaci na Maza da Mata don Yada Musulunci

  • Sanata Shehu Buba Umar ya gina katafaren masallaci, makarantar islamiyya da wurin ibada na musamman domin mata a jihar Bauchi
  • Shehu Buba ya gode wa Allah bisa kammala aikin, yana mai cewa ya gina masallacin ne domin taimakawa wajen yada musulunci
  • Malaman da suka halarci bude masallacin sun yaba wa sanatan bisa yadda yake taimakon addini, wanda hakan zai amfane shi a lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Sanatan da ke wakiltar Mazabar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Buba Umar, ya gina katafaren Masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyyaa ranar Juma'a.

Sanata Shehu Buba ya yi wannan babban aiki ne a unguwar Nabordo, hedkwatar Masarautar Jema’a da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Masallacin Juma'a.
Katafaren masallacin Juma'a da Sanata Shehu Buba Umar ya gina a jihar Bauchi Hoto: Shehu Buba Umar
Source: Facebook

Sanatan Bauchi ya gina masallacin Juma'a

Leadership ta rahoto cewa aikin ya ƙunshi masallacin Juma’a, masallacin sallar mata, makarantar islamiyya, da ban-dakuna a cikin harabar masallacin.

Kara karanta wannan

An cafke jami’in DSS da ake zargi ya tursasa wa budurwa barin Musulunci bayan dirka mata ciki

Da yake jawabi jim kaɗan bayan bude masallacin, wanda ya gudana bayan sallar Juma’a, Sanata Shehu Buba ya ce ya yi aikin ne domin bunƙasa ilimin addinin Muulunci da ƙarfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma.

Ya buƙaci masu ibada da su ci gaba da yi wa Jihar Bauchi da ƙasar nan baki ɗaya addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali.

Sanatan ya bayyana cewa akwai ayyukan jin ƙai da yake aiwatarwa a fadin mazabarsa da ma wajen ta, domin tallafa wa rayuwar talakawan ƙasa.

Sanata Shehu Buba ya jinjina wa Sarkin Jema'a

Sanata Buba ya kuma yaba wa mutanen masarautar Jema’a bisa zaman lafiya da fahimtar juna, inda ya danganta hakan da shugabanci na adalci da gaskiya na Sarkin Jema’a, Alhaji Suleiman Bala Suleiman.

Ya ce salon shugabancin Sarkin na taka rawa wajen inganta haɗin kai da zaman lafiya tsakanin addinai a masarautar da ma jihar baki ɗaya.

A cewarsa, gina masallatai da yake yi a ciki da wajen mazabarsa ya samo asali ne daga burinsa na taimakawa wajen yaɗa Musulunci da kuma neman lada a lahira.

Ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa ba shi damar aiwatar da abin da ya bayyana a matsayin sadaka, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanatan Najeriya ya gina danƙareren gida, talakawa sun masa rubdugu a intanet

Sanata Buba ya kuma gode wa malamai da sauran masu ruwa da tsaki bisa ƙarfafawa da goyon bayan da suka bayar, wanda ya taimaka wajen nasarar kammala aikin.

Sarki da malamai sun yabi Sanata Buba

A nasa jawabin, Sarkin Jema’a, Alhaji Suleiman Bala Suleiman, ya gode wa Sanata Shehu Buba Umar bisa wannan aiki, tare da roƙon Allah Ya saka masa da alheri mai yawa.

Sanata Shehu Buba.
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar dattawa, Shehu Buba Umar Hoto: Shehu Buba Umar
Source: Facebook

Wasu malamai da suka yi magana a wajen taron sun bayyana Sanata Buba a matsayin Musulmi nagari wanda ke kula da addininsa da kokarin yiwa kansa tanadin lahira.

Sun kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da shi ta hanyar zuba jari a ayyukan da ke amfanar addini da al’umma.

Sanata Buba ya yi maganar takarar gwamna

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Buba Umar ya bayyana cewa zai amsa kiran al'ummar Bauchi, kungiyoyin siyasa da ke neman ya fito takarar gwamna a zaben 2027.

Sanata Buba ya kuma nuna cewa duk da cewa yana wakiltar Bauchi ta Kudu ne kadai, amma yana kallon kansa a matsayin mai wakiltar muradun jihar baki daya.

Shehu Buba, wanda ake ganin yana takun saka da Gwanna Bala Mohammed, ya ce lokacin kamfe bai yi ba, amma zai sanar da matsayarsa idan lokaci ya yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262