Harin Amurka: Shugaban Ƙaramar hukuma a Binuwai Ya Nemi Ɗauki kan Karuwar Ƴan Ta'adda

Harin Amurka: Shugaban Ƙaramar hukuma a Binuwai Ya Nemi Ɗauki kan Karuwar Ƴan Ta'adda

  • Shugaban ƙaramar hukumar Agatu a Binuwai ya bayyana bukatar neman dauki game da karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankinsa
  • Rahotanni sun ce ‘yan bindigar da suka tsere daga Sokoto bayan harin Amurka sun kutsa cikin al’ummomin Agatu, suna kashe mutane da lalata dukiyoyi
  • Shugaban ƙaramar hukumar ya soke yarjejeniyar kiwo ta 2017 tare da umartar makiyaya su fice daga Agatu nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Benue– Shugaban ƙaramar hukumar Agatu, James Ejeh, ya bayyana cewa an samu ɓullar sabon salon munanan hare-hare da ke faruwa a al’ummomin yankinsa.

James Ejeh ya bayyana cewa wannan ya biyo bayan luguden wutar da Amurka ta kai kan ‘yan bindiga a jihar Sakkwato, lamarin da ya sa suka yi hijira zuwa yankinsa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kutsa har fadar sarki suka sace mutane

Ana zargin yan ta'adda sun karu a Agatu ta jihar Binuwai
Wasu daga cikin dakarun Najeriya a bakin aiki, Gwamna Hyancith Alia Hoto: HQ Nigerian Army/Fr Hyancith Lormen Alia
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa, koken na kunshe a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda James Ejeh ya ce akwai bukatar kawo masu dauki.

An samu karuwar yan ta'adda a Binuwai

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa al'umomin yankin ne suka fara ƙorafin cewa ana kai masu hare-hare, tare da neman agaji domin ceto rayuwarsu.

A cewar sanarwar Shugaban ƙaramar hukumar:

“A halin yanzu ƙaramar hukumar na fuskantar sabon guguwar hare-haren tashin hankali da ake zargin ‘yan bindiga dauke da makamai ne suka aikata, kuma mun yi imanin cewa wannan sakamakon luguden wutar sojoji ne da aka yi a yankin Sakkwato.”

An ruwaito cewa a ranar Kirsimeti, 25 ga Disambar 2025, Amurka ta kai hari ta sama kan ‘yan ta’addan ISWAP da ake zargin suna da sansani a dazukan Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa wannan hari ya tarwatsa ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta masu barin maboyarsu zuwa wasu yankuna daban-daban, kuma suna ci gaba da kai hari.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi watsi da hukuncin kotu game da shugabancin jam'iyyar a Kano

An soke kiwo a karamar hukumar Binuwai

Da yake ƙarin bayani, Ejeh ya ce ‘yan bindigar da ke tserewa daga yankunan makwabta sun kutsa cikin al’ummomin Agatu, inda suka haddasa mummunan tashin hankali ga fararen hula marasa galihu.

An kori Fulani makiyaya daga karamar hukuma a Binuwai
Taswirar jihar Binuwai mai fama da rikice-rikice Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce hare-haren sun haifar da asarar rayuka, jikkata mutane da dama, rahotannin fyade, lalata gidaje da gonaki, tare da tilasta wa daruruwan mazauna gudun hijira cikin tsoro da rashin tabbas.

A cewarsa:

"Wannan lamari babbar matsalar jin kai da tsaro ce da ke bukatar daukar matakin gaggawa.”

Ya koka kan yadda ake ci gaba da zubar da jini a Agatu, yana mai cewa ana farautar mutanensa a kan ƙasarsu ta gado ba tare da wani dalili ba.

Biyo bayan, Shugaban ƙaramar hukumar ya sanar da soke yarjejeniyar 2017 da ta bai wa makiyaya damar yin kiwo a Tsibirin Adepati.

Ya ce yarjejeniyar ba a aiwatar da ita da gaskiya ba, kuma ta jefa al’ummar Agatu cikin mummunan hali, don haka ya ayyana ta a matsayin wacce ba ta da amfani.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: An tabbatar da mutuwar kasurgumin 'dan bindiga a Najeriya

Ejeh ya umarci makiyaya dauke da makamai da su fice daga ƙasar Agatu nan take, yana mai jaddada cewa babu wani yanki a ƙaramar hukumar da aka ware wa makiyaya.

Ya ce Agatu al’umma ce ta noma, kuma dole ne a kare gonaki domin tabbatar da wadatar abinci da rayuwar jama’a. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su tura karin sojoji da ‘yan sanda yankin.

Binuwai : Sojoji sun kama dan ta'adda

A baya, mun wallafa cewa sojoji sun cafke wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga da hukumomin tsaro suka dade suna nema bisa zargin hannu a manyan laiffuka a yankin Arewa ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa an dade ana bibiyar wanda aka kama saboda zargin hannu a ayyukan garkuwa da mutane da fashi da makami, musamman a kan iyakar jihohin Binuwai da Taraba.

Sojojin Najeriya da ke aiki a yankunan karkara na Benue da Taraba sun kara kaimi wajen kakkabe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, domin dawo da zaman lafiya da ba al’umma damar ci gaba da harkokinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng