2027: Tinubu Ya Ware Sama da Naira tiriliyan 1 domin Harkokin Zabe

2027: Tinubu Ya Ware Sama da Naira tiriliyan 1 domin Harkokin Zabe

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware sama da Naira tiriliyan 1 ga hukumar INEC a kasafin kuɗin 2026 domin fara shirin babban zaɓen 2027
  • Kasafin kudin ya nuna an yi tanadin kuɗin tun da wuri, abin da INEC ta dade tana nema domin samun cikakkiyar damar gudanar da zaɓe
  • Rahotanni sun nuna cewa dokar zaɓen Najeriya ta 2022 ta wajabta sakin kuɗin zaɓe ga INEC akalla shekara guda kafin babban zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware kuɗi har Naira tiriliyan 1.013 ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, a cikin kasafin kuɗin 2026 da aka miƙa wa Majalisar Tarayya.

Bayanai sun nuna cewa wannan mataki na zuwa ne a matsayin shiri na musamman domin sharar fagen gudanar da zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

ADC na shirin hadaka da PDP da NNPP domin kifar da Tinubu a 2027

Shugaba Bola Tinubu da wasu masu zabe
Shugaban kasa Bola Tinubu da masu zabe. Hoto: Bayo Onanuga|INEC Nigeria
Source: Facebook

Rahoton AIT ya nuna cewa kudin da aka ware wa INEC na daga cikin kasafin kuɗin ƙasa baki ɗaya da ya kai N58.18 tiriliyan, wanda gwamnatin Bola Tinubu ta amince da shi a bana.

Bola Tinubu ya ware wa INEC N1.013tn

A cikin cikakken bayani kan kasafin, gwamnatin tarayya ta kiyasta samun kuɗin shiga da yawansu ya kai N34.33tn, yayin da jimillar kuɗin da za a kashe suka kai N58.18tn. Daga ciki, an ware N15.52tn domin biyan bashi.

Tribune ta rahoto cewa bayanai daga takardun kasafin kuɗin 2026 da Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya ya fitar sun nuna cewa adadin kuɗin da aka ware wa INEC ya kai N1,013,778,401,602.

An ce ware kuɗi ga hukumar INEC mai yawa a kasafin shekarar 2026 na nuna muhimmancin da gwamnati ke bai wa shirya zaɓe tun kafin lokaci.

Dokar zaɓe da batun sakin kuɗin INEC

Dokar Zaɓe ta 2022 ta fayyace buƙatar sakin kuɗin zaɓe ga INEC tun da wuri. Sashe na 3, sakin layi na 3 na dokar ya tanadi cewa dole ne a saki dukkan kuɗin da suka shafi babban zaɓe ga INEC ba daga baya ba sai shekara guda kafin gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan

INEC ta matso da nesa kusa, ta fadi abin da zai sa ta samu nasara a zaben 2027

Wannan tanadi na doka ya kasance wani ginshiƙi da INEC ke jingina da shi wajen neman kuɗi a kan lokaci, domin gujewa matsalolin da suka taso a zaɓukan da suka gabata.

Saboda haka aka ce ware sama da Naira tiriliyan 1 a kasafin 2026 na iya ba hukumar damar fara shirye-shiryen zaɓen 2027 ba tare da tsaiko ba.

Shugaban hukumar zabe ta kasa
Shugaban hukumar zabe ta INEC na wani bayani. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

INEC ta dawo rajistar masu zabe

A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta sanar da fara rajistar masu kada kuri'a a fadin kasa baki daya a zagaye na biyu na shirin.

Hakan na zuwa ne bayan hukumar zabe ta kammala zagaye na farko na shirin rajistar 'yan kasa a shekarar 2025 da ta gabata.

Kamar yadda aka yi a zagayen farko na shirin, hukumar INEC ta sanar da cewa za a cigaba da yi wa mutane rajista ta yanar gizo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng