Kasafin Kudin 2026: Biliyoyin da Aka Ware don Tafiye Tafiyen Tinubu, Shettima

Kasafin Kudin 2026: Biliyoyin da Aka Ware don Tafiye Tafiyen Tinubu, Shettima

  • A watan Disamban 2025, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2026 ga majalisar tarayya
  • A cikin kasafin kudin an ware makudan kudade don tafiye-tafiyen Mai girma Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
  • Hakazalika a cikin tiriliyoyin da za a kashe, an ware kudade masu kauri don sayo sababbin motocin da za a rika aiki da su a fadar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 6.14 domin tafiye-tafiyen kasashen waje na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Bisa ga kasafin da aka gabatar, an kara Naira miliyan 873.88 domin tafiye-tafiye na cikin gida, wanda ya kai jimillar kuɗin tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu zuwa Naira biliyan 7.01.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki motar sufurin gwamnati, an harbe mutane

An ware kudade don tafiye-tafiyen Tinubu da Shettima
Shugaban kasa Bola Tinubu na gaisawa da mataimakinsa Kashim Shettima Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, kasafin ya tanadi Naira biliyan 1.73 domin tafiye-tafiye da harkokin sufuri.

Tafiye-tafiyen Tinubu, Shettima za su lashe biliyoyi

Wannan ya haɗa da Naira miliyan 417.48 na tafiye-tafiye na cikin gida da kuma Naira biliyan 1.31 na tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.

Takardun kasafin sun nuna cewa kuɗaɗen tafiye-tafiyen kasashen waje na shugaban kasa da mataimakinsa suna karkashin sashe na ayyukan fadar shugaban kasa.

Jimillar kuɗin da aka ware a wannan sashe sun haɗa da Naira biliyan 8.38 don ayyukan fadar shugaban kasa, da kuma Naira biliyan 2.64 don ayyukan fadar mataimakin shugaban kasa a kasafin 2026.

Tafiye-tafiye da lantarki a fadar shugaban kasa

A wani muhimmin tanadi kuma, fadar Shugaban kasa ta ware Naira biliyan 7 domin sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A shekarar 2024, Shugaba Tinubu ya rage yawan jami’an da ke yi masa rakiya a tafiye-tafiyensa na cikin gida da na kasashen waje da kashi 60 cikin 100.

Kara karanta wannan

Hajji: Gwamnatin Tinubu za ta tatsi harajin N5.4bn, an fadi yadda maniyyaci zai biya

A kasafin shekarar 2024, Tinubu da Shettima sun shirya kashe Naira biliyan 8 gaba ɗaya wajen tafiye-tafiye na cikin gida da na kasashen waje.

Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2026

Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 58.18 na shekarar 2026 ga majalisar tarayya a ranar 19 ga Disamba, 2025, bayan samun amincewar majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).

A ranar 23 ga watan Disamba, 2025, majalisar dattawa ta amince da kasafin don karatu na biyu.

A halin yanzu, kasafin shekarar 2026 na ci gaba da fuskantar binciken ’yan majalisa, inda ake sa ran za a yi muhawara mai zurfi kan rabon kuɗaɗen, musamman duba da matsin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta.

An warewa Tinubu biliyoyi don tafiye tafiye a 2026
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na dago hannu a saman jirgi Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Za a sayo wa fadar shugaban kasa motoci

Kasafin kudin ya kuma nuna cewa fadar shugaban kasa na shirin kashe Naira biliyan 3.3 domin saya da sauya motocin aiki a shekarar 2026, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Cikakken bayani ya nuna cewa an ware Naira biliyan 2.56 don sayen motocin aiki na fadar shugaban kasa, Naira miliyan 768.9 domin sauya motocin SUV.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Sai kuma Naira miliyan 115.4 kuma domin tayoyin motocin kariya daga harsasai, motocin aiki na yau da kullum, motocin daukar marasa lafiya da sauran motocin aiki.

Ba a damu da talaka ba

Sahabi Abdulrahman ya koka kan yadda gwamnati take ware kudade kan abubuwan da ba za su amfani talaka ba.

Ya shaidawa Legit Hausa cewa ko kadan bai kamata a ce za a sayo wasu motoci ba don amfanin fadar shugaban kasa.

"Ko a shekarar da ta gabata an sayo motoci, to menene amfanin sake ware wasu kudin domin sayo sababbi."
"Tabbas ana kashe kudade ta hanyar da ba ta dace ba a kasar nan."

- Sahabi Abdulrahman

Kudin da aka warewa tsofaffin shugabannin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ware kudade masu kauri don biyan hakkokin shugabannin Najeriya a kasafin kudin shekarar 2026.

Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 2.3 a cikin kasafin kuɗin 2026 domin biyan haƙƙoƙi da alawus-alawus na tsofaffin shugabannin Najeriya da mataimakansu.

Waɗanda za su ci gajiyar kuɗin suka haɗa da Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, Janar Ibrahim Babangida, Janar Yakubu Gowon, da Janar Abdulsalami Abubakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng