Sarkin Musulmi Ya Nemi Tinubu Ya Ziyarci Garin da aka Yi wa Jama'a Yankan Rago a Neja
- Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara Kasuwar Daji bayan kisan fararen hula
- JNI ta ce halin tsaro na kara tabarbarewa a jihohi da dama, lamarin da ke haddasa fushi da damuwa ga talakawa, musamman a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2027
- Kungiyar ta kuma yaba da hare-haren sama da sojojin sama suka kai kan ‘yan ta’adda, tana mai kira da a dauki matakai masu karfi da gaggawa domin dakile matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya ziyarci Kasuwar Daji da ke Borgu a jihar Neja.
JNI ta ce irin wannan ziyara za ta taimaka wajen kwantar da hankalin jama’a da kuma hana yiwuwar daukar fansa bayan kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Source: Facebook
A sakon da fadar Sarkin Musulmi ta wallafa a Facebook, JNI ta ce kisan da aka yi a Kasuwar Daji ya kara tayar da hankalin jama’a, musamman ganin yadda irin wadannan hare-hare ke yawaita a sassa daban-daban na kasar nan.
Kiran Sarkin Musulmi ga Bola Tinubu
A cikin sanarwar da Sakatare Janar na JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar, kungiyar ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi a Kasuwar Daji, tare da tuna makamantan hare-hare da suka faru a jihohin Borno, Katsina, Kebbi, Kwara, Sokoto da Zamfara.
Kungiyar JNI ta ce wannan yanayi na bukatar zurfin nazari, musamman ganin cewa babban zaben kasa na 2027 na kara matsowa.
Ta bayyana cewa kisan Kasuwar Daji na daga cikin jerin abubuwan da za a iya kauce musu idan an dauki gargadi da shawarwarin da aka bayar a baya da muhimmanci.
A kan haka ne kungiyar ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya ziyarci yankin tare da yin jawabi na musamman domin kwantar da hankalin jama'a.
Leadership ta rahoto cewa JNI ta kuma gargadi gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, domin ‘yan ta’adda na kara matsowa yankin, suna fakewa da dazuzzuka.
Wani rahoton da tashar DW Hausa ta wallafa ya nuna cewa 'yan bindigar da suka farmaki jama'a sun musu yankan rago a kasuwar.
Kira ga gwamnati da hukumomin tsaro
Duk da matsin halin tsaro, JNI ta yaba wa gwamnatin tarayya, musamman sojojin sama, bisa hare-haren da aka kai kan ‘yan ta’adda a wasu sassan jihohin Neja, Kwara da Zamfara.
Kungiyar ta ce irin wadannan matakai na kara karfafa gwiwar jama’a, amma ta bukaci a ci gaba da su ba tare da sassauci ba.
JNI ta bayyana damuwarta kan yadda ake ci gaba da rasa rayukan fararen hula, tana tambayar tsawon lokacin da ‘yan kasa marasa laifi za su ci gaba da fuskantar kisa ba tare da dalili ba.

Source: Facebook
Kungiyar ta bukaci gwamnati da ta hukunta duk wani jami’i da aka samu da sakaci a aikinsa, tare da karfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro domin kawo karshen dukkan barazanar tsaro.
Haka kuma, JNI ta jaddada bukatar tattara makamai a hannun ‘yan ta’adda, tare da gaggauta tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa, wadanda da dama daga cikinsu suka zama ‘yan gudun hijira a kasarsu.
Najeriya ta saye jiragen yaki a Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun kai ziyarar aiki na musamman Amurka, inda suka shafe kwanaki.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta yi magana game da wasu jiragen yaki da Najeriya ta saya a wani kamfani na Amurka da ake shirin kawo su.
Lura da halin da kasar ke ciki, tawagar Najeriya ta bukaci gaggauta kawo jiragen domin samun damar kakkabe 'yan ta'adda masu kai hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


