Tinubu Ya Yi Albishir ga ’Yan Najeriya game da Tsadar Kayan Abinci a 2026

Tinubu Ya Yi Albishir ga ’Yan Najeriya game da Tsadar Kayan Abinci a 2026

  • Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya yi hasashe game da farashin kayan abinci yayIn da aka shiga sabuwar shekarar nan da aka shiga
  • Tinubu ya yi albishir ga yan kasa cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a shekarar, yana cewa ana iya saukowa ƙasa a 2026
  • Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan sauyi zai inganta rayuwar jama’a tare da hanzarta bunƙasar tattalin arzikin Najeriya baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake kwantarwa yan Najeriya hankali game da hauhawar farashin kayan abinci.

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na shirin fuskantar raguwar hauhawar farashin kaya sosai a shekarar 2026.

Tinubu ya yi alkawarin saukar da farashin kayan abinci
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Dalilan da suka jawo sabon rikici tsakanin Fubara da Wike

Kokarin gwamnatin Tinubu kan tsadar abinci

Hakan na zuwa ne yayin da yan kasar ke kokawa game da tsadar kayayyaki musamman na abinci.

Gwamnatin na ci gaba da yi wa yan Najeriya alkawarin cewa za su kawo karshen lamarin inda ta ke cewa matsala ce mai wucewa.

Ko a kwanaki baya, Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga kwamitin majalisar zartarwa ta kasa domin daukar matakai kan farashin abinci.

Umarnin ya mayar da hankali ne wajen tabbatar da tsaro da saukin jigilar kayan gona a manyan hanyoyi domin rage kudin sufuri.

Karamin Ministan harkokin noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka bayan kammala wani taro a birnin tarayya Abuja.

Tinubu ya fadi yadda za su karya farashin abinci a 2026
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Alkawarin da gwamnatin Tinubu ta yi

Onanuga ya ce da ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki, ana sa ran hauhawar farashin kaya za ta iya sauka ƙasa da kashi 10 cikin ɗari.

“Lallai, hauhawar farashin kaya na iya sauka zuwa ƙasa da kashi 10 cikin ɗari kafin ƙarshen wannan shekara.”

Kara karanta wannan

Malami ya fadi manyan Najeriya 3 da za su tilasta wa Atiku janye wa Jonathan

- In ji Bayo Onanuga.

Ya kara da cewa hakan zai haifar da ingantacciyar rayuwa da saurin bunƙasar tattalin arziki, yana mai cewa shekarar 2026 za ta kasance shekara mai tarihi.

Shugaban ya yaba wa kamfanoni da masu zuba jari, bayan kasuwar hannayen jari ta Najeriya ta kai darajar Naira tiriliyan 100.

Rahotanni sun nuna kasuwar ta rufe a Naira tiriliyan 101.80, lamarin da Tinubu ya bayyana a matsayin abin ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari.

Ya bukaci ’yan Najeriya su zurfafa zuba jari a cikin tattalin arzikin cikin gida, yana tabbatar da cewa “shekarar 2026 za ta samar da ribar da ta fi girma.”

Tinubu zai sake karbo jiragen yaki daga Amurka

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatinsa wurin tabbatar yaki da ta'addanci domin wanzar da zaman lafiya.

Tinubu ya ce Najeriya ta sayi jiragen yaƙi huɗu masu saukar ungulu daga Amurka, waɗanda za su iso ƙasar nan nan gaba kaɗan.

Shugaban ya ce matsalar tsaro ta kai matakin damuwa a duniya, lamarin da ya jawo haɗin gwiwa da ƙasar Amurka domin kawo karshen ta'addanci da ke faruwa musamman a yankin Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.