An Bankado Masu Basaja da Sunan Babban Hafsan Sojan Najeriya

An Bankado Masu Basaja da Sunan Babban Hafsan Sojan Najeriya

  • Rundunar Sojin Najeriya ta gargaɗi jama’a kan karuwar shafukan bogi a kafafen sada zumunta da ke amfani da sunan shugabanta
  • Ta jaddada cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ba shi da kowane asusun sada zumunta a hukumance
  • Bayan gano asusun, rundunar ta ce ta fara ɗaukar matakan kama masu ƙirƙirar asusun domin mika su gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da jama’a cewa ta lura da karuwar shafukan bogi a kafafen sada zumunta da wasu marasa gaskiya ke ƙirƙira.

Mutanen da ke samar da shafukan na bayyana kansu a matsayin masu wakiltar ko kuma suna da alaƙa da Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Buratai ya maka tsohon soja a kotu, ya nemi diyyar N1bn

Sojoji sun ce wasu bata-gari na amfanin da sunan shugaban rundunar tsaron Najeriya
Shugaban rundunar sojan kasa, Laftanar Janar Waidi Shaaibu Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A sakon da Zagazola Makama ya wallafa a shafin X, rundunar ta bayyana cewa irin waɗannan shafukan ba su da sahihanci, kuma ana amfani da su ne domin yaudara da yaɗa ƙarya.

Rundunar sojin Najeriya ta gargadi jama'a

A cewar sanarwar, sojoji sun nuna damuwa matuƙa kan yadda wasu ke ƙoƙarin ruɗar jama’a ta hanyar amfani da sunan babban hafsan tsaro ko na rundunar sojin Najeriya domin karɓar kuɗi.

Sanarwar da Kanal Appolonia Anele, Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, ya sanya wa hannu ta ce haka kuma mutanen na neman tallafi na ƙarya ko yaɗa bayanan da ba su dace ba.

Saboda haka, an buƙaci jama’a da su kasance masu taka-tsantsan tare da gujewa mu’amala da duk wani shafi da ke ikirarin wakiltar Babban Hafsan Tsaro a kafafen sada zumunta.

Rundunar soji na binciken asusun bogi

Rundunar Sojin Najeriya ta jaddada cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa ba shi da wani shafukan sada zumunta a hukumance a kowane dandali.

Kara karanta wannan

Sunan Matawalle ya fito a zargin cafke hadimin Gwamna Dauda, APC ta yi magana

Sojoji sun gargadi jama'a kan masu amfani da sunan Laftanal Janar Shaaibu Waidi
Babban hafsan tsaron kasa a Najeriya, Laftanal Janar Shaaibu Waidi Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Ta ce saboda haka, duk wani saƙo, sanarwa ko buƙata da ake dangantawa da shi a shafukan sada zumunta to ƙarya ce tsagwaronta.

An shawarci jama’a da kada su amsa saƙonni, su tura bayanai ko kuma su raba duk wani abu da ya fito daga irin waɗannan shafukan bogi.

Haka kuma, sojoji sun ja hankalin jama’a da su sanar da hukumomin da suka idan suka ci karo da irin waɗannan shafuka, domin a dakile ayyukan yaudara tun da wuri.

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa tana ɗaukar dukkannin matakan da suka dace domin gano tare da kama masu sarrafa shafukan bogin.

Dakarun sojin Najeriya sun samu nasara

A baya, mun wallafa cewa sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara bayan sun hallaka ‘yan bindiga 23 a wasu hare-haren hadin gwiwa da suka gudana a iyakokin jihohin Kano da Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa an kai wadannan hare-hare ne tsakanin ranakun 1 zuwa 2 ga watan Janairun 2026, a wani yunkuri na ci gaba da murkushe ‘yan bindiga da ke addabar yankunan Arewa maso Yamma.

Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke kara zage damtse wajen amfani da sahihan bayanan sirri domin dakile ayyukan ta’addanci a dukkanin sassan kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng