Najeriya za Ta shigo da Jiragen Yaki daga Amurka don Murkushe 'Yan Ta'adda

Najeriya za Ta shigo da Jiragen Yaki daga Amurka don Murkushe 'Yan Ta'adda

  • Gwamnatin tarayya da kamfanin Bell Textron na Amurka sun kaddamar da shirin gaggauta kawo jiragen yaki AH-1Z guda 12 domin karfafa tsaron Najeriya
  • Manyan jami’an rundunar sojin sama sun gana da jami’an kasar Amurka a San Diego, inda suka tattauna kan kalubalen dabaru da jadawalin isar da jiragen
  • Ana sa ran jiragen yakin za su taimaka matuka wajen yaki da ta’addanci a Najeriya, tare da rage asarar fararen hula da kuma karfafa hadin gwiwar kasa da kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Rundunar Sojin Saman Najeriya ta bayyana cewa tana aiki kafada da kafada da gwamnatin Amurka da kamfanin Bell Textron domin gaggauta karɓo jiragen yaki AH-1Z guda 12.

Taron bitar shirin gudanarwa da aka yi daga 5 zuwa 6, Janairu, 2026, ya tattaro manyan jami’an rundunar sojin saman Najeriya, jami’an gwamnatin Amurka da wakilan kamfanin Bell Textron.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara shirin tsige gwamna Fubara bayan sabon rikici da Wike

Sojojin Najeriya da Amurka yayin taro
Sojan Najeriya da Amurka bayan magana kan jiragen yaki. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

Rundunar sojojin ta wallafa a Facebook cewa taron ya mayar da hankali kan duba warware matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya tsawon shekaru.

Dalilin gaggauta karɓo jiragen daga Amurka

A cewar bayanan rundunar sojin sama, shirin sayen jiragen AH-1Z yana daga cikin manyan matakan sabunta kayan aikin yaki domin bai wa rundunar damar kai hare-hare da kyau da kuma tallafa wa dakarun kasa.

An bayyana cewa jiragen na dauke da na’urorin kai farmaki na zamani, wadanda ke bai wa sojoji damar kai hari sosai, tare da rage illa ga fararen hula.

Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya ce rundunar za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an kawo jiragen Najeriya cikin kankanin lokaci.

Alakar Najeriya da Amurka kan tsaro

Shugaban rundunar ya bayyana godiya ga gwamnatin Amurka da Bell Textron bisa yadda suka nuna gaskiya da kwarewa wajen tafiyar da shirin.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fadi yadda yawan gwamnoni zai taimaki Tinubu a 2027

Punch ta wallafa cewa ya ce sayen jiragen ba kawai shirin sabunta kayan aiki ba ne, har da alamar karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.

A cewarsa, wannan hadin gwiwa na nuna nauyin da kasashen suka dauka tare wajen tabbatar da tsaro a yankin da ma duniya baki daya.

Sojojin Najeriya da wasu 'yan Amurka
Dakarun sojojin saman Najeriya da jami'an kasar Amurka. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Source: Facebook

Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar sojin sama ba tare da tangarda ba.

An jaddada cewa shirin ya dace da burin Najeriya na inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan da hare-haren ’yan ta’adda suka fi kamari.

Tarihin sayen jiragen Amurka da darajarsu

Najeriya ta samu amincewar gwamnatin Amurka tun a watan Afrilu, 2022, domin sayen jiragen AH-1Z guda 12 a karkashin tsarin sayen kayan yaki na kasashen waje. Darajar jiragen ta kai Dalar Amurka miliyan 455.

Daga bisani, a ranar 12, Maris, 2024, aka bai wa Bell Textron kwangilar kerawa da isar da jiragen. Tun daga lokacin ake gudanar da shirye-shiryen fasaha da dabaru domin tabbatar da cewa an kammala aikin yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Ana fargabar yaki bayan Amurka ta tabo Rasha, gwamnatin Putin ta magantu

Trump na iya kawo sabon hari Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka za ta iya kawo sabon hari Najeriya a kan zargin kashe Kiristoci.

Trump ya bayyana cewa ya so harin da ya kawo a karon farko ya magance matsalar tsaro, amma kuma ya ga alamun sai ya kara kawo sababbin hare-hare.

A maganar da ya yi a wannan karon, shugaban Amurka ya ce ana kashe Musulmai a Najeriya kamar yadda hadiminsa ya fada a Oktoban 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng