CBN Ya Yi Hasashen yadda Farashin Fetur zai Kasance a Najeriya a Shekarar 2026

CBN Ya Yi Hasashen yadda Farashin Fetur zai Kasance a Najeriya a Shekarar 2026

  • Babban Bankin Najeriya ya yi hasashen yadda farashin man fetur zai ci gaba kasancewa a shekarar 2026, duk da sauye-sauyen da ake samu a kasuwar mai a cikin gida
  • Hasashen ya dogara ne kan yanayin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, musayar kuɗin kasashen waje da kuma yawan man da ake samarwa a Najeriya a kullum
  • Saukar farashin man fetur da matatar Dangote ta janyo a baya na iya fuskantar barazana, idan aka samu koma baya a samar da mai ko kuma aka koma dogaro da shigo da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa farashin man fetur a Najeriya na iya ci gaba da kasancewa a kusan N950 kan kowace lita a shekarar 2026, bisa sabon hasashen tattalin arziki da ya fitar.

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana kan Musulmin Najeriya yayin barazanar kawo hare hare

Bankin ya bayyana hakan ne a cikin hasashensa na tattalin arzikin Najeriya na 2026, inda ya yi la’akari da wasu muhimman abubuwa da ke shafar farashin mai, ciki har da farashin danyen mai a duniya.

Mutane na sayane mai a gidan mai
Yadda ake sayen fetur a wani gidan mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CBN ya wallafa hasashen ne a shafin yanar gizo a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke jin sauƙin farashin man fetur bayan matatar Dangote ta rage farashi a ƙarshen 2025, lamarin da ya tilasta wa gidajen mai sauke farashinsu.

Mene ne hujjojin CBN wajen hasashen kudin fetur

CBN ya ce hasashensa na lita a kan N950 ya dogara ne kan zaton cewa farashin danyen mai zai kai Dala 60 kan kowace ganga a ƙarshen 2025, sannan ya sauka zuwa kusan Dala 55 a shekarar 2026.

Punch ta rahoto cewa bankin ya yi hasashen cewa musayar kuɗin waje za ta daidaita a nan gaba, inda Dala ɗaya za ta kasance a kan kusan N1,400 a 2026.

A cewar bankin, ana sa ran daidaituwar kasuwar canjin kuɗin waje, ƙarin masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma bunƙasar ayyukan tattalin arziki za su taimaka wajen rage matsin lamba kan farashin fetur.

Kara karanta wannan

NLC ta yi wa Tinubu barazana saboda a dakatar da dokokin haraji

Duk da haka, hasashen ya nuna cewa farashin man fetur zai ci gaba da kasancewa sama da yadda ake samunsa a halin yanzu.

Tasirin samar da danyen mai a cikin gida

Hasashen ya kuma nuna cewa Najeriya za ta ci gaba da samar da kusan ganga miliyan 1.5 na danyen mai a kullum a shekarar 2026. Wannan adadi, a cewar CBN, na da matuƙar muhimmanci wajen daidaita farashin fetur a cikin gida.

CBN ya jaddada cewa ci gaba da tace mai a cikin gida na taka rawar gani wajen rage dogaro da shigo da fetur daga waje, lamarin da kan haddasa tashin farashi.

Matatar Dangote mai tace mai a Najeriya
Wani bangaren matatar Dangote da ke tace mai a gida Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Babban bankin ya yi nuni da cewa, idan aka koma shigo da mai kacokan, farashin fetur na iya yin tashin gwauron zabi a fadin Najeriya.

CBN ya kuma bayyana cewa ana sa ran farashin makamashi a duniya zai ragu da kusan kashi 6.99 a shekarar 2026, sakamakon saukar farashin danyen mai.

NNPCL ya sauke farashin mai a Abuja

A wani labarin, mun kawo muku cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya rage farashin man fetur a wasu gidajen mai na mallakarsa.

Kara karanta wannan

An hango jirgin yakin Amurka ya sauka a Najeriya da dare

Rahotanni sun bayyana cewa masu sayen mai sun tabbatar da rage farashin da kamfanin ya yi a wasu sassan birnin tarayya Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan matatar Dangote ta rage kudin litar mai a kwanakin baya, wanda ke tilasta wa 'yan kasuwa sauke farashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng