Kotun ICC Ta Umarci Sake Duba kan Hukuncin Nnamdi Kanu? Gaskiya Ta Fito
- Rahotanni na yawo a kafafen sadarwa cewa Babbar Kotun Tarayya za ta sake duba hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu a Abuja
- Sai dai an yi bincike mai zurfi game da jita-jitar da ake yadawa cewa za a sake duba kan hukuncin da aka yankewa shugaban IPOB
- Hakan ya biyo bayan Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci bayan tuhumar Nnamdi Kanu da ta'addanci a Abuja a shekarar bara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An yi ta yada wasu rahotanni cewa babbar kotun tarayya za ta sake duba kan hukuncin da aka yankewa Nnamdi Kanu kan zargin ta'addanci.
Rahoton ya ce wai Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya watau ICC ce ta ba da wannan umarni domin sake duba hukuncin da aka yi a ranar 20 ga watan Nuwambar 2025.

Source: Twitter
Jita-jitar sake duba shari'ar Nnamdi Kanu
Sashen binciken gaskiya na TheCable ya karyata ikirarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa akwai yiwuwar sake duba hukuncin.
A rahoton, an ce kotun tana shirin sake duba hukuncin da zaman gidan yari da aka yanke wa Nnamdi Kanu.
Wasu wallafe-wallafe da suka bazu a kafofin sadarwa sun yi ikirarin cewa Mai Shari'a James Omotosho zai sake nazarin hukuncin ne saboda matsin lamba daga Amurka da Isra’ila.
Kafafen sada zumunta irin su @vdmempire sun wallafa wannan labari da sauran wurare iri ɗaya, kamar an yi kwafa ne kawai aka yada shi.
Har ila yau, @JohnEzeakolam ma ya wallafa rahoto makamancin wannan inda ya ce ana shirin sake yin duba kan hukuncin da aka yanke.
A cikin saƙon, an ce:
“Yanzu: Mai shari’a James Omotosho na shirin sake duba shari’ar Mazi Nnamdi Kanu… ICC ta ba da umarnin a sake duba hukuncin.”

Source: Twitter
Binciken da aka yi kan jita-jitar
Bincike da aka yi a shafin yanar gizo da kafofin sada zumunta na ICC domin tabbatar da ko kotun ta yi wani bayani kan shari’ar Kanu da aka yi a Abuja.
Amma binciken ya nuna cewa ICC ba ta yi wani sharhi ko bayani ba kan hukuncin da aka yanke masa, babu wani sahihin gidan jarida da ya ruwaito cewa ICC ta nemi a sake duba hukuncin.
Haka kuma, babu wata hujja da ke nuna cewa Mai shari’a Omotosho na shirin sake duba hukuncin da ya yanke a watan Nuwamba 2025.
A tsarin shari’ar Najeriya, wanda aka yanke wa hukunci yana da damar kai ƙara zuwa Kotun Daukaka Ƙara da kuma Kotun Koli.
A wannan yanayin, har yanzu Kotun Daukaka Ƙara ba ta yanke hukunci ba, don haka ba abu ne da aka saba gani ba kotu ta sake duba hukuncin da ta riga ta yanke.
Kotu ta amince a dauke Kanu daga Sokoto?
An ji cewa Nnamdi Kanu da ke zaman daurin rai da rai ya mika bukatar a sauya masa wajen zama daga Sokoto zuwa Abuja.
Nnamdi Kanu ya tunkari kotu da bukatar hakan ne domin a cewarsa Sokoto ta yi nisa sosai da Abuja kuma ba zai samu damar daukaka karar yadda ya kamata ba.
Alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho, ya fadi dalilin kin amincewa da bukatar tare da bayyana cewa sai an ji ta bangaren gwamnatin tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


