Nasara daga Allah: An Tabbatar da Mutuwar Kasurgumin Dan Bindiga a Najeriya
- An tabbatar da mutuwar wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi jama'a, Terkaa Samuel a musayar wuta a jihar Benuwai
- Rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunta, DSP Udeme Edet ta fitar a Makurdi
- Haka zalika 'yan sanda sun kai dauki bayan samun labarin barkewar rikici tsakanin wasu 'yan daba, inda aka kama mutane takwas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Benuwai ta tabbatar da mutuwar wani kasurgumin ɗan bindiga mai suna Terkaa Samuel.
'Dan bindigar, wanda ya yi kaurin suna wajen addabar mutane da hare-haren ta'addanci, ya fito ne daga garin Jandekyula da ke ƙaramar hukumar Wukari a Jihar Taraba.

Source: Twitter
Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis a Makurdi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yadda aka kashe hatsabibin dan bindiga
Udeme Edet ta ce an harbi ɗan bindigar ne a ranar Laraba a yankin Zaki-Biam, da ke ƙaramar hukumar Ukum ta jihar Benue, yayin musayar wuta da jami’an tsaro.
A cewar ta, rundunar ta samu bayanan sirri cewa wasu ’yan bindiga sun kai farmaki da nufin sace wani mai otal a yankin.
Mai magana da yawun 'yan sandan ta ce nan take bayan samun rahoton, aka tura tawagar sintiri daga ofishin ’yan sanda na Ukum zuwa wurin.
“Lokacin da ’yan bindigar suka hango jami’an ’yan sanda, sai suka buɗe musu wuta, jami’ai suka mayar da martani da karfi, inda ɗaya daga cikin ’yan bindigar ya samu mummunan rauni,” in ji Edet.
Yan sanda sun kwato makamai
Ta ce a yayin samamen, jami’an tsaro sun kwato bindiga da aka ƙera a gida, alburusai biyu da kuma jakar layu daga hannunsa, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
"An garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Zaki-Biam, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa. Daga bisani aka gano cewa shi ne Terkaa Samuel, wanda ya shahara wajen aikata fashi da garkuwa da mutane," in ji Edet.

Source: Facebook
'Yan sanda sun kama 'yan daba a Benuwai
A wani lamari daban, Edet ta ce a wannan rana ɗaya, jami’an ’yan sanda daga caji ofis din Jato-Aka sun shiga tsakani a rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin daba biyu, Red da Black.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, yayin da wasu da dama suka jikkata, aka kai su asibitoci domin samun kulawa.
Ta ce jami’an sun cafke mutane takwas da ake zargi, tare da kwato bindiga ƙirar gida guda ɗaya, fankom harsashi da aka yi amfani da shi, gatari biyu da adduna biyu.
Nasarorin 'yan sanda kan miyagu a Kano
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta kama mutane fiye da 3,000 da ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane da ayyukan daba a shekarar 2025.
Hakan ya nuna yadda rundunar ta baza komarta a dukkan sassan jihar domin kakkabe ɓata-garin da ke neman jefa jihar cikin rashin zaman lafiya.
Rundunar ta kuma yi nasarar ƙwace makamai masu yawa da suka haɗa da bindigogin AK-47 guda 9, ƙananan bindigogi 84, da harsashai 198 da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

